Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene ne Halascin Rike Alkur'ani A Bayan Liman Kana Dubawa Yayin Da Ake Sallahr Tahajjud?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne halascin riƙe alƙur'ani a bayan liman kana dubawa yayin da ake sallahr tahajjud?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Rike alƙur'ani abayan liman da wannan manufar ya saɓawa sunnah, saboda ababe kamar haka;

1- Yana hana mutum sanya hannunsa na dama a kan hagu akirjinsa, ayayin da yake tsaye.

2- Yanasa mutum motsi maiyawa a cikin sallah, wanda ba'a da bukatarsa shi ne buɗe Alƙur'ani, da rufeshi da sanyashi karkashin hammata.

3- Yana shagaltar damai sallah wajan budashi.

4- Yana hana mai sallah yadunga kallan inda yake saka goshinsa, mafiya yawan malamai suna ganin kallan inda kake sujjada sunnah ne kuma shi ne ya fi falala.

5- Sau dayawa wani lokacin mutum yakan iya mantawa a cikin sallah yake, idan baya halartowa zuciyarsa cewa yana cikin sallah, saɓanin idan yana cikin kushu'i yasanya hannunsa nadama a kan nahagu aƙirjinsa, yasunkwui dakansa yana kallan inda yake sujjada, hakan zaifi kusa wajan halartowar zuciyarsa cewa sallah yake kuma yana bayan liman.

Shaik Muhammad Salihi Al'Usaimeen Mujallatul da'awa (1771/45).

Dan haka wannan bashi da asali a cikin addini, saboda fadin Allah maɗaukakin sarki:

وإذا قرئ القرآن فاستمعوا  له وأنصتوا لعلكم ترحمون، الأعراف

 Idan ana karanta Alƙur'ani ku nutsu kusaurara ku ji danku samu rahama.

Dafadinsa Allah maɗaukakin sarki:

قد أفلح الموؤمنون الذين هم في صلاتهم خاشعون.

Tabbas muminai sun rabauta, su ne waɗanda asallarsu suke tsoran Allah.

Da fadin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam (Ansanya muku limami danku yi koyi dashi, idan ya yi kabbara ku yi kabbara, idan yana karatu ku yi shiru kusaurari karatun.

WALLAHU A'ALAM.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/K7RkƘRMf2b57l3UENoJ1Or

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments