Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Cin Abincin Lokacin Kiran Sallah, Hudowar Alfijir Yayin Ɗaukar Azumi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Da Yawa Daka Cikin Mutane Suna Cin Abinci Lokacin da Ladan Yake Kiran Sallar Hudowar Alfijir Har Yagama Kiran Sallah, Ina Hukuncin Cin Wannan Abincin Lokacin Kiran Sallah?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Hukuncin wannan cin abincin lokacin da liman yake kiran sallah saboda kiran sallar ladani, idan ladanin yakasance baya kiran sallah sai bayan yasami yakinin hudowar Alfijir, abunda yake wajibi shi ne mutum yakame daka cin abinci daka lokacin dayaji kiran sallah, saboda fadar Annabi sallallahu Alaihi wasallam :

"Ku ci ku sha harsai kunji ibnu ummu maktuum yakira sallah" Idan kuma ladani baya samun yakinin hudowar alfijir yana amfani da lokacine, to abunda ya fi shi ne kamewa daka cin abinci idan akayi kiran sallah, mutum zai iya cin abinci har ladani yagama kiran sallah matukar bashi da yakinin hudowar alfijir yana aiki da lokacine, domin asali shi ne wanzuwar dare, sai dai abunda ya fi shi ne mutum ya yi tsaka tsakiya, kada ya ci abinci bayan kiran sallar hudowar Alfijir.

Mauƙi'i Shaik Muhammad Salih Al'usaimin.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments