Dukiyoyin da ake fitarwa da Zakka kashi biyu ne:
Akwai waɗanda suke fitattu
ne, an san su. Ko dai saboda su ake yawan faɗa a bayanin zakka;
ba afaɗar nau’o’in da ke
cikin su.
Ko kuma saboda su
babu saɓanin malamai a
kansu.
Akwai kuma waɗanda ba fitattu
ba, Ko dai saboda ba ayawan fito da su a bayani, ko kuma saboda malamai sun yi
saɓani a kan su.
FITATTUN
DUKIYOYIN ZAKKA
Dukiyoyin da akafi sani yayin da akayi maganar zakka
sune:
• Zakkar kuɗi.
• Zakkar dabbobi.
• Zakkar amfanin
gona.
• Zakkar ma’adanai
da binanniyar dukiyar jahiliyya.
• Zakkar dukiyar
ciniki.
ZAKKAR KUƊI:
Asalin kuɗi dai, kamar yadda
muka sani, su ne zinariya da azurfa. Ko dinare da dirhami.
A yanzu kuwa, su ne kuɗaden da ƙasashe kan buga, domin a rinƙa amfani
dasu a duk duniya.
Ko kuma a iya ƙasashen kad'ɗai, kamar dai
Dalar Amurka da Nairar Najeriya.
Malamai sun haɗu a kan wajabcin
Zakka a kan zinariya da azurfa, koda kuwa ba abuga su a matsayin kuɗi ba.
Kamar a ce suna
asalin siffarsu, ko an ƙara wani mazubi dasu, ko an yi wani
abin ado dasu, bana mata ba.
Za a fitar da zakka daga zinariya (Gold) Idan nauyin ta
ya kai nauyin giram (85).
Sai a fitar da
kashi biyu da rabi cikin ɗari 2.5% Wato a kasa gida arba’in 40 sai a ɗauki kaso ɗaya shi ne zakkar ɗaya cikin arba'in
1/40 shi kuma dinare wato bugagge, idan yakai dinare ashirin, sai a fitar da ɗaya bisa huɗu na dinare ɗaya.
Ita kuwa azurfa
idan nauyin ta yakai giram (595), sai a fitar da kashi biyu da rabi cikin ɗari 2.5% Wato a
kasa gida arba’in 40 sai a ɗauki kaso ɗaya shi ne zakkar 1/40.
Shi kuma Dirhami
wato bugagge idan ya kai Dirhami ɗari biyu, sai a fitar da Dirhami biyar.
Sai dai kamar
yadda muka sani, duka biyun wato Dinare da Dirhami yanzu ba aamfani dasu a
matsayin kuɗi.
Don haka abin da
musulmi suka yi a ƙasashensu shi ne, sukan ɗauki nisabin ɗayansu ne su
kimanta kuɗin ƙasarsu da shi.
Amma zaifi dacewa
ayi kimar da Dinare (Zinariya). Saboda dalilai kamar haka:
1• Malamai sunce kimar Dirhami tana iya canzawa, daga
lokaci zuwa lokaci, ba kamar yadda take a zamanin Annabi {s.a.w} ba, shi kuwa
Dinare bai canza ba.
2• An kwatanta nisabin dinare anga ya fi zama kusa dana
dabbobi dana amfanin gona.
[Duba FiKhuz-Zakat, juz’i na 1, sh:256 – 264]
Ke nan yadda
zakkar dukiya take shi ne idan dukiyarka takai nisabi ko ta huce saika
lissafata ka kasa kaso arba’in 40, sai ka fitar da kaso ɗaya daga ciki shi
ne zakkar ɗaya bisa arba'in 1/40.
ALLAH shi ne mafi sani.
ALLAH ka ba mu ikon
aiki da abin da muka karanta.
ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.