Ticker

6/recent/ticker-posts

Mace ce ta mutu ana bin ta bashin azumi, tana da 'ya'ya, ya halatta a biya mata azumin?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mace ce ta Mutu Ana binta bashin Azumi tanada 'ya'ya, ya halatta Abiya mata Azumin?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wanda yabar Azumi Saboda Uzurin tafiya ko rashin lafiyar da'ake tsammanin Warkewarta, Wajibine yarama Azumin, idan ya mutu batareda ya rama Azumin ba, tareda cewa yasamu dama, azumin yana nan Akansa.

Ana so Majibintansa 'yan'uwansa najini su rama masa, saboda Hadisin Aisha Allah yakara mata yarda daka manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya ce:( Wanda ya Mutu Ana binsa Azumi, waliyyinsa yai masa Azumin, ) Bukahri (1952) da Muslim (1147).

Amma Idan ya Mutu kafin ya samu damar rama azumin, kamar wanda cuta ta same shi bata warkeba harya mutu yana cikinta, Babu komai Akansa ba za a rama masaba.

Wanda Kuma sakaci da wasa da dokokin Allah ya sa yabar Azumi baiyiba, kuma Babu wani uzuri dayasa yabar Azumin, ba za a rama masaba, Shi ma in ya rama ba za a karɓa ba kuma Ana binsa Azumin.

Saboda wucewar lokacin Azumin.

Saboda Haka ya halatta 'ya'yanta Su rama mata azumin, ko da kuwa kowa cikin 'ya'yanta kowa zaiyi uku ko dai-dai yanda zai musu saukin rama mata.

WALLAHU A'ALAM.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IƙsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments