Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin ya halatta yin sallar wutiri bayan asuba idan mutum bai samu ya yi a cikin dare ba?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin ya halatta yin sallar wutiri bayan asuba idan mutum bai samu ya yi a cikin dare ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Lokacin sallar wutiri yana karewa daketowar alfijir saboda fadin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam (sallar dare raka biyu-biyuce, idan dayanku yana tsoran kada ya kasa farkawa ya yi raka'a ɗaya saita zamto masa wutirin Abunda yasallah ta)

Bukhari (472)

Muslim yaruwaito hadisi daka Abu Sa'idul khudry Allah yakara masa yarda daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (ku yi wutiri kafin sallar Asuba) Muslim (754)

Imamu Ahmad yafitar dahadisi daka Abu dauda da turmuzi hakim ya ingantashi daka karijata bin huzafa Allah yakara masa yarda ya ce: ( Lallai Allah ya baku wata sallah wacce tafi muku Alkhairi samada jajayen rakuma, sai sahabbai sukace ya manzan Allah wacce sallah ce? sai ya ce: wutiri tsakanin sallar isha'i zuwa hudowar alfijir.

Idan Akayi kiran Sallar Assalatu Mutum bai samu damar ya yi wutiri ba zaijinkirtashi zuwa lokacin sallar walaha saiya sallaci abunda yasawwaka agareshi, raka'a biyu ko huɗu ko sama da haka, yanda Al'adarsa take, idan kasaba raka'a uku kake da daddare bakasamu kayiba darana zakayi raka'a huɗune sallama biyu, idan raka'a biyar kake to inzaka ramata da rana raka'a shida zakayi sallama uku, haka mutum zai auna yadunga lura dayanda yasaba dakuma ƙa'idar yanda zaiyi idan darana zai rama, domin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yakasance yanayin wutiri da raka'a goma sha daya, idan wani Abu yashagaltar dashi da daddare bai yiba baccine ko rashin lafiya ko wani Abun, idan zairamata darana yanayin raka'a goma shabiyune, haka A'isha Allah yakara mata yarda tace kamar yanda Bukhari da Muslim Suka ruwaito wannan kuma shi ne shari'a koyi da Annabi Sallallahu Alaihi wasallam.

Maj-mu'u fatawa Bin baaz (11/300)

Kamar yanda a wani wajan Shaik Bin baaz yasake fada a cikin majmu'u fatawa dinsa (11/305- 308)

Hakama shaik Usaimeen yabayyana a cikin maj-mu'u fatawa dinsa (14/114)

Hakika yatabba wasu jama'a daka cikin sahabbai sun ce babu laifi mutum ya yi sallar wutiri bayan ketowar Alfijir harzuwa tayar da sallar asuba, daka cikinsu akwai ibnu mas'ud Nisa'i yaruwaitoshi (1667) Albani ya ingantashi a cikin sahihun nisa'iy. da Ibnu Abbas malik yaruwaito a cikin Muwadda (255) da Ubada bin Sãmit malik yaruwaito a cikin muwadda (257) Allah yakar yarda da su baki daya.

Shaikul Islam Ibnu taimiyyah Allah yajikansa darahama ya ce: Wanda bacci ya dauke shi bai yi wutiri ba zaiyishi daka hudowar alfijir zuwa sallar asuba, kamar yanda Abdullahi Dan Umar ya aikata haka da A'isha dasauransu, Abu dauda yaruwaito hadisi daka Abiy sa'idul khudry ya ce: Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (wanda ya yi bacci bai yi wutiri ba koya manta bai yiba ya sallace shi idan yawayi gari koya tuna) ruwaya tasa6a daka Ahmad shin zai rama shafa'i tare da uwutiri? Ingantacciyar magana shi ne zai ramashi tare da shafa'i, hakika ya inganta daka Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Wanda bacci yadaukeshi bai yi wutiriba koya manta bai yiba yasallaceshi idan yatuna, wannan lokacin da daya tuna koya tashi daka bacci shi ne lokacinsa) wannan yashafi sallar wajibi da kiyamullaili da wutiri da Nafiloli ratibai.

Duba fatawa Kubra (2/240).

Duk wanda mutum ya yi dai-daine, idan ya rama wutiri kafin atayarda sallar asuba yayi, idan kuma yabari sai bayan rana tafito ta washe lokacin sallar walaha shi ma babu laifi.

Abisa wannan yahalatta rama sallar wutiri bayan Sallar Asuba sai dai idan darana za ka rama to sai dai kayi shafa'i ban da wutiri bazakayi raka'a ɗaya tilo kayi sallama ba.

WALLAHU A'ALAM.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments