Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Musulunta A Watan Ramadan

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Idan mutum ya musulunta acikin watan Ramadan, shin ya wajaba akansa ya azumci sauran kwanakin da suka rage na watan, tun daga ranan da ya musulunta har zuwa ƙarshen watan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Eh Idan mutum ya musulunta acikin watan Ramadan to yana wajaba akansa ya azumci sauran kwanakin da suka rage na watan, tun daga ranan da ya musulunta har zuwa ƙarshen watan, wannan ijma'ine na malamai, ibnu Ƙudama Allah ya masa rahama ya ambaci wannan ijma'in. Amma kwanakin da suka wuce na watan Ramadan din kafin musuluntarsa ba zai ramasu ba, wannan shi ne zancen jumhur na malamai daga cikin su harda malaman mazhabobi guda huɗu. Domin kwanakin da suka shuɗe sun kasance ne alokacin yana halin kafirci, misalinsu shi ne kamar misalin watanni Ramadan da suka shuɗe ne kafin musuluntarsa.

 Amma idan musuluntar nasa ta kasance da rana ne to wajibine ya kame bakinsa har zuwa faduwar rana Sannan kuma ya rama azumin wannan wunin bayan Ramadan, domin ya riski wani ɓangare na ibada alokacin da ya musulunta hakan sai lizimta masa ramata kamar wanda ya musulunta lokacin sallah bai fita ba.

WALLAHU A'ALAM

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments