Ticker

6/recent/ticker-posts

Idan Ke Ce Budurwar Wa Za Ki Zaɓa?

 Wata budurwa ce ana sauran sati guda aurenta, sai mijinta ya turo mata saƙo cewa: "Ki yi haƙuri, ba zan samu damar aurenki ba. Yanzu haka nan da sati biyu za a ɗaura mini aure da Laraba." Ita kuwa larabar babbar ƙawar budurwar ne.

Ba a jima da yin haka ba sai aka aiko wai ana kiran ta a waje. Fitar ta ke da wuya sai ta tarar da baban saurayin ne ya zo wurinta. Kuma ya zo ne damagar yana so ya aure ta. Ta koma gida domin ta yi shawara.

Jimawa kaɗan kuma sai aka sake kiran ta daga waje. Da ta fito sai ta ga baban ƙawarta Laraba ne ya zo. Shi ma yana so ya aure ta.

Idan ke ce yaya za ki yi? Za ki auri baban saurayinki da ya guje ki ne, ko za ki auri baban ƙawarki da ta ƙwace miki saurayi?

Za ku iya rubuta ra'ayoyinku a sashen comment da ke ƙasa.

Post a Comment

0 Comments