Gazal, kamar yadda wannan muƙala ta Hausance kalmar ghazal, ɓangare ne ko wani nau’in waƙa wanda asalinsa daga adabin Larabci yake. Farkonsa wani ƙaramin gutsure ne na wani nau’in waƙar da ake kira ƙasiidah. Sannu a hankali gazal yana jan hankalin mawaƙa har dai a ƙarni na bakwai (Miladiyya) ya samu babban tagomashi a sanadin bunƙasar ilmi wanda Musulunci ya haifar. Wannan gutsuren ƙasida ya ci gaba da bunƙasa har sai da ya samu zama mai cin gashin kansa, ya zama waƙar gazal, wadda ba ‘yar rakiya ba. Waƙar ta samu tagomashi babba har wasu al’ummomi suka sadu da ita suka maishe ta tasu.
Gudale Waƙar Soyayya: Misalin Gazal (Ghazal) Cikin Rubutattun Waƙoƙin Hausa
Abdullahi Bayero Yahya
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Email: bagidadenlema2@gmail.com
Phone: 07031961302
TSAKURE
Gazal,
kamar yadda wannan muƙala ta Hausance kalmar ghazal, ɓangare ne ko wani nau’in waƙa wanda
asalinsa daga adabin Larabci yake. Farkonsa wani ƙaramin
gutsure ne na wani nau’in waƙar da ake kira ƙasiidah. Sannu a
hankali gazal yana jan hankalin mawaƙa har dai
a ƙarni na bakwai (Miladiyya) ya samu babban tagomashi a sanadin bunƙasar ilmi wanda Musulunci ya haifar. Wannan gutsuren ƙasida ya ci gaba da bunƙasa har
sai da ya samu zama mai cin gashin kansa, ya zama waƙar gazal, wadda ba ‘yar rakiya ba. Waƙar ta
samu tagomashi babba har wasu al’ummomi suka sadu da ita suka maishe ta tasu. Ganin yadda wannan
nau’i na waƙa ya samu karɓuwa a faɗin duniya shi ya sa wannan muƙala ta yi ƙoƙarin ta
gano ko akwai shi a rubutattun waƙoƙin Hausa, waɗanda
tushensu daga na Larabci ne. Muƙalar ta
lura cewa akwai shi har kashi biyu cikin waƙoƙin Larabci: gazal na cikin ƙasida da
gazal mai cin gashin kansa. To amma dangane da rubutattun waƙoƙin Hausa, muƙalar ta keɓe kanta
ga kashi na biyu da ta kira ‘gazaliya
ko gudale’. Ta kawo
waƙar Alƙali Alhaji Haliru Wurno mai suna
Gudale, wadda ya yi ga Alhaji Giɗaɗo Ibrahim
Yabo, a matsayin kyakkyawan misali na rubutattar waƙar gazaliya ta Hausa.
1.1 Gabatarwa
Rubutattun waƙoƙi ɓangare ne
na adabin Hausa wanda tushensa daga rubutattun waƙoƙin Larabci ne. Kafin Hausawa su sadu da Larabawa da addinin
Musulunci, ba su da irin wannan ɓangare cikin adabinsu. Da yake waɗanda suka ƙirƙiro
rubutattun waƙoƙi cikin
adabin Hausa malamai ne kuma masana a fannin addinin Musulunci da adabin
Larabci, sai rubutattun waƙoƙin Hausa suka ɗauko nau’o’i da sigogi, har ma da salailai irin na waƙoƙin Larabci, musamman waɗanda a ganinsu za su dace da
manufofinsu na addini. Saboda haka ne wasu daga cikin waɗannan suka fi saura yawa a adabin
Hausa. Misali, akwai waƙoƙin Hausa
na wa’azi da na
madahu birjik, kamar wada ayyukan Hiskett da Ɗangambo
da Yahya suka nuna.[i] Haka kuma
akwai waƙoƙin addu’a da na furu’a da na nasiha da makamantan haka.[i]
Akwai kuma wasu nau’o’in da waɗannan malamai, magabata suka aro ma adabin Hausa. Sai dai waɗannan nau’o’i ba su cika yawa ba. Wasu kuma ba duk ɗalibin waƙa ya damu da su ba, watakila saboda rashin sanin tarihinsu da na
tunanin da akan sa wajen tsara su.
To daga cikin irin waɗannan waƙoƙi da ma ɓangarorin tsarinsu akwai abin da
ake kira ‘ghazal’ da
Larabci. Wannan muƙala za ta tattauna ne kan wannan
tsari ko nau’i na waƙoƙin Larabci da muƙalar take iƙirarin cewa lalle akwai shi a waƙoƙin Hausa, aƙalla daga mawaƙan da
suka naƙalci adabin Larabci musamman waƙoƙinsa da tarihinsu. An kawo wannan
nazari da bayani ne ba don begen jiya ba. A’a, sai dai don a fahimci mufari, a gane yadda wasu abubuwa suka
faro domin kada a yi musu mummunar fahimta har a kai ga liƙa wa wannan nau’i da ake kira ghazal na waƙoƙin Hausa abin da ba nasa ba, har
ruɗu ya kai
ga shiga dangane da shi a nazari.[i] Haka
kuma ghazal yana nan bai mutu ba a waƙoƙin Larabci, har ma a yau wasu al’ummomi kamar na Turai sun are shi. Kada watan
wata rana a ɗauka cewa ghazal daga can
tushensa yake!
2.1 Ghazal Da Asalinsa A Waƙoƙin Larabci
Kalmar ghazal, daga harshen Larabci tushenta yake
wanda ke nufin bayyana so ko ƙauna ta
hanyar magana ga wanda ko wadda ake so; musayar magana ta soyayya da wanda ko
wadda ake so.[i] A fagen waƙa kalmar tana nufin, wani nau’in waƙa ne da ke bayyana tsananin raɗaɗin ciyon rashi ko rabuwa a ɓangare guda, da kuma matsanancin kyawo na masoyi ko masoyiya duk a
lokaci guda.[i]
Tarihin ghazal ya faro ne tun a wajajen ƙarni na shida (ƙ. 6),
wato a zamanin Jahiliyyah. A
lokacin shi ghazal kashi ko ɓangare ne na daɗaɗɗiyar irin waƙar nan ta cikin waƙoƙin Larabci wadda ake kira ƙasiida. Ƙasiida waƙa ce da ake tsarawa mai kashi
uku, kowane kashi na bin wani ba tare da zaren tsarin ya tsinke ba, amma kuma
kowane kashi yana ɗauke da
saƙo ko jigo dabam. Waɗannan kashe-kashe su ake kira:
a) Nasiib
b) Rahiil
c) (ɗaya daga sanannun jigogi a wancan zamani na Jahiliyyah, kamar
yabo <madiih> da darasi<hikam> da zambo <hija’>
da alfahari ko wasa kai <fakhr>)
Za a lura da cewa ba a ambaci kashin ghazal ba.
To shi bai cikin manyan kashe-kashe. A cikin kashin farko yake, wato nasiib. Akwai
abubuwan da kashin nasiib kan ƙunsa. Da
farko, a jumlace kuma cikin taƙaitawa,
ana iya cewa ibn Ƙutaibah[i] ya bayyana ma’anar ƙasida a wurin
Larabawa[i] kamar haka:
Mawaƙi zai fara waƙarsa ta ƙasiida yana mai ambaton ƙasarsa ta
haihuwa da kuma abubuwan da suka shuɗe cikinta. A nan zai yi juyayin waɗannan abubuwa tare da yin kira ga abokan tafiya da su tsaya (su
saurare shi ya ambaci mutanen da suka yi rayuwarsu a ƙasar). Daga nan ne mawaƙin zai
tsunduma cikin nasiib inda yake juyayin raɗaɗin soyayyarsa, da raɗaɗin rabuwa
da masoyi/masoyiya, da bege da matsanancin son da yake yi ga
masoyinsa/masoyiyarsa. Dalilin yin wannan magiya dangane da masoyi/masoyiya shi
ne, sanin cewa begen mata abu ne da ke manne ga zukatan maza…
Idan mawaƙi ya kai nan, ya san ya tattara
hankalin masu saurare. Sai ya shiga cikin rahiil, inda yake juyayin wahalar tafiya, kamar
rashin samun kwana na yawan darairai da kuma zafin rana.
A kashi na uku ne da ke biye, mawaƙi zai
shiga cikin ainihin jigon waƙarsa.
Idan yabo ne yake son ya yi ga wani to a wannan sashin ne zai fara shi. Idan
kuma zambo ne ko wasa kai ko darasi, duk dai a wannan sashi ne zai fara shi.[i]
2.2 Bunƙasar
Ghazal Da Yaɗuwarsa A
Sauran Adubban Duniya
Da wannan tsari ne waƙar da Larabawa ke kira ƙasiidah ta ci gaba da kasancewa har sai
bayan da Musuluinci ya bayyana kuma ilmi ya watsu a ƙasashen Musulunci sakamakon Alƙur’ani da hadissan Manzo (s.a.w.). Kafin zamanin
bunƙasar ilmi da saduwar adabin Larabci da wasu al’ummomi kamar Farisa da Pakistan da Afirka da
sauransu, ghazal bai tashi daga zama wani ɓari na kashin nasiib cikin waƙar ƙasiidah ba. To
amma da ilmi ya bunƙasa sanadiyyar nazarin Alƙur’ani da
Hadissai da kuma cuɗanya da
wasu al’ummomin
da Musulmi suka kai, sai waƙar ghazal ta
samu zama mai cin gashin kanta. Hakan kuma ya auku ne musamman a zamanin
Khilafar Umayyah (daga 661 zuwa 750) da farkon Khilafar Abbasiyyah (daga 750
zuwa 1258). A lokacin ne kowane kashi na waƙar ƙasiidah ya zamo nau’i mai cin gashin
kansa. Cikin waɗannan
kuwa har da nau’in ghazal
wanda ya samu tagomashi daga mawaƙa. A
halin da ake ciki, ba a ƙasashen gabas ta tsakiya da na
gabas mai nisa da na Afirka kurum waƙar ghazal ta kutsa
ba, har ma cikin ƙasashen Turai da na Amerika waƙar ta miƙe ƙafa.
Hasali, yadda ta samu karɓuwa ta
bunƙasa a nahiyoyin Asiya da Afirka, haka ta samu a Turai da Amerika
tun a ƙarni na 19, farko a Jamus sannan
sauraan ƙasashe da harsuna kamar Ingilish.[i]
A tsawon zamani, tun daga ƙarni na bakwai har zuwa ƙarni na
13, waƙar ghazal ta ci gaba da samun bunƙasa, har ya kasance aka karkasa ta zuwa nau’o’i dabam daban, kama daga nau’in da ya shafi yabon masoyiya wadda ta zamo hakin-sama ga mawaƙi har zuwa ga nau’in da ke
zayyana jikin mace. Waƙar ta kasance nau’in da muhimmin jigonta shi ne, nuna
matsananciyar ƙauna zuwa ga masoyiya ko masoyi.
Malamai, musamman na zuhudu da sufanci su suka fi yin ghazal cikin waƙoƙin da suke yi na yabon Allah ko
wani shugabansu. A ƙasar Hausa irin wannan ghazal aka
fi yi tun cikin ƙarni na 18 da na 19.
3.1 Ghazal A Ƙasar
Hausa
Za a lura da cewa a adabin Larabci, ghazal ya
faro daga kasancewa wani ɗan rakiya
cikin waƙar da ake kira ƙasida tun a zamanin Jahiliyya, har ya rikiɗe zuwa lokacin da likkafarsa ta
yi gaba daga ƙarni na bakwai ya zamo mai cin
gashin kansa a madadin ɗan
rakiya.
To a wannan ɓangare ne wannan muƙala za ta
Hausance kalmar ghazal zuwa
‘gazal’. Za ta kuma bambanta tsakanin gazal na cikin waƙar ƙasida da kuma gazal zunzurutunsa,
wato mai zaman kansa wanda kai tsaye mawaƙi ya
bayyana soyayya a matsayin babban jigon waƙarsa.
Gazal na cikin ƙasida zai ci gaba da amsa sunan
asali, wato ‘gazal’. Ita kuwa waƙar gazal
mai cin gashin kanta ta amsa sunan ‘gazaliya’ ko ‘gudale’. Ga taƙaitaccen bayani kan kowace waƙa:
a) Gazal: baitocin da ke nuna tsananin soyayya da raɗaɗin rabuwa da masoyi ko masoyiya, wadda aka saka cikin waƙar ƙasida a matsayin baitoci ‘yan rakiya kamin shiga cikin babban jigon waƙar ta ƙasida.
b) Gazaliya/Gudale (ba ‘gazaliyyat’ ta harshen Larabci da ke nufin
jumlar gazal ba!): waƙar da aka tsara gaba ɗayanta tana bayyana tsananin so
ga masoyi ko masoyiya, wani lokaci har da bayani kan raɗaɗin rabuwa ko yin nisa da masoyi/masoyiya
Kamar wada sauran ƙasashen da suka rungumi Musulunci sai adabin Larabci ya yi tasiri
kan nasu adabin, haka adabin Hausa ya samu. Abin nufi a nan shi ne, bayan da
Hausawa suka karɓi
Musulunci sai hanyoyin neman ilmi, da irin ilmin shi kansa, da kuma adabinsu,
ko dai suka sauya ko kuma suka samu tasiri daga waɗanda zuwan na Musulunci ya kawo.
Misali, karatu a makaranta da samuwar rubutattar waƙa duka Musulunci ya kawo su. Ya kawo juyin-juya-hali daga neman
ilmi ta hanyar tatsuniya da barantaka gun mai sana’a, zuwa makarantar allo da makarantar sani
har ma da barantakar.[i]
Lokacin da Hausawa suka yi
zurfi ga samun ilmin addinin Musulunci, suka zurfafa cikin sanin adabin
Larabci, musamman cikin ƙarni na 18 da na 19, a zamanin
Shehu Usmanu ɗan
Fodiyo, sai nau’in gazal
ya samu shiga cikin rubuce-rubucen mallaman zamanin, amma fa waɗanda suka rubuta cikin harshen
Larabci. A binciken da mai muƙala ya yi
sai a ƙarshen ƙarni na 19 ne aka fara samun waƙar gazal
ko gazaliya cikin harshen Hausa. A sannan ɗin ma waƙa ɗaya tak manazarta suka gano. Waƙar gazal
da baitocin gazal sun zauna daram cikin waɗanda waɗannan
malamai suka rubuta da Larabci a duk tsawon ƙarni na
18 da na 19. Misali, a waƙar da Shehu Usmanu ɗan Fodiyo ya rubuta cikin Larabci
yana yabon Sayyid Mukhtar al-Kunti, akwai gazal a baitocin farko. Haka kuma
Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya rubuta gazal. Junaidu (1985) yana ganin cewa
a ƙarni na 19, Muhammadu Buhari ne, (ɗan uwan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello), daga cikin marubutan ƙarni na 19 ya fi kowa rubuta gazal. Rubuta gazal cikin harshen
Larabci a ƙarni na 19, abu ne wanda, kamar
yadda Sambo Wali Junaidu ya yi nuni[i],
tabbas ya auku ne saboda babbar manufar da mallaman zamanin suka sa a gaba.
Wato manufar jaddada addinin Musulunci a ƙasar
Hausa. Ba su bukatar su cusa sha’awar waƙoƙin
soyayya ga zukatan mabiyansu a madadin samun ilmin addini. To da yake waƙoƙi cikin harshen Larabci a wancan
lokacin sai waɗanda suka
yi zurfi cikin harshen ke iya fahimtar waƙoƙin da aka rubuta cikin harshen, sai suka keɓe gazal cikinsa.
A iyakar binciken mai
wannan muƙala, sai a ƙarni na 20 ne waƙoƙi gazaliya cikin harshen Hausa suka yawaita, duk kuwa da cewa a ƙarshen ƙarni na 19 an samu waƙar gazal ɗaya
cikinsa.[i] Marubuta waƙoƙi biyu, Sa’adu Zungur da Mu’azu Haɗeja, duk sun rubuta gazal cikin wasu waƙoƙinsu, duk da cewa manazarta za su
iya su kalli gazal ɗin a
matsayin gabatarwa cikin waƙoƙi biyu na waɗannan
marubuta. Waƙoƙin dai su
ne ‘Arewa
Jumhuriya Ko Mulukiya’[i] ta Zungur da ‘Tutocin Shehu Da Waninsu’ ta Haɗeja. Waƙoƙin duka biyu suna ɗauke da babban jigo na siyasar
Nijeriya, amma a farkonsu sai marubutan suka kawo jigon da ke bayyana ɓurɓushin ƙauna ga sarakunan Arewa. Bayan
wannan sai marubutan suka shiga babban jigon siyasar Nijeriya tare da nuna haɗarin da ke ƙalubalantar Arewa. To idan aka yi la’akari da bayanin da ya gabata cikin wannan muƙala za a lura da cewa duka waƙoƙin nan biyu na Zungur da Haɗeja waƙoƙin da ake
kira ƙasida ne. Baitocinsu na farko
kuwa suna cikin ‘nasib’ na tsarin ƙasida.
Haka nan kuma cikin nasib ɗin ne
gazal yake.
To amma a ra’ayin wannan
muƙala, waƙar da kai tsaye za a iya a kira ‘gazal’ ko ‘gazaliya’
ita ce waƙar Alƙali Alhaji Haliru Wurno wadda ya kira ‘Gudale’.[i] Wannan waƙa ita ce za a gabatar a matsayin misali na yadda marubuta waƙoƙin Hausa, musamman masu zurfin
ilmin waƙoƙin
Larabci, suke sanya gazal cikin waƙoƙinsu. Sai dai shi Haɗeja waƙarsa muhammasa ce, ba ‘yar ƙwar bibbiyu ce saɓanin
yadda ƙasida da gazal na Larabci suke
ba.
4.1 GUDALE:Waƙar Yabon Alhaji Giɗaɗo Ibrahim
Yabo
4.1.2Bayanin Diddigin Waƙa
Marubucin wannan muƙala ya samo wannan waƙa daga
hannun marubucinta a shekarar 1986, kuma kamar yadda mawaƙin ya saba, ya rera ta a gabansa, a ƙofar
gidansa cikin garin Wurno. A wannan lokaci yana mallamin Arabiyya da addini a
makarantar Sakandare ta Wurno. Shugaban makarantar shi ne Alhaji Giɗaɗo Ibrahim Yabo. Haliru ya sheda wa marubucin nan cewa wannan
shugaba ya nuna masa ƙauna da girmamawa ainun. Ya ba
shi duk irin goyon bayan da malami ke bukata don ya gudanar da karantarwar da
aka sa shi ya yi. Saboda haka ba abin mamaki ne ba a ga Haliru Wurno ya tsara
waƙa musamman don nuna ƙauna ga
wannan shugaban makaranta.
Babu tabbacin shekarar da
aka yi wannan waƙa sai dai ana iya ƙiyastawa, cewa a cikin shekarun da Alhaji Giɗaɗo yake shugaban kwalejin horar da malamai ta garin Wurno ne aka
tsara ta, kuma Haliru yana karantarwa a lokacin. Wannan lokaci kuwa shi ne,
tsakanin 1981 da 1988.
Waƙar ‘yar
tagwai ce mai baiti ɗari cif
cif. Tana da amsa-amon ciki da na waje. Wato ƙarami da
babba wanda ba ya sauyawa tun daga baiti na ɗaya har zuwa na ɗari.
Wannan babban amsa-amo kuwa shi ne, ‘ni’. Waƙar ta samo sunanta ne daga kalmar ‘gudale’ da aka yi salon kinaya
da ita. Gudale dai ita ce nagge fara, kyakkyawa, mai babbar hantsa, wadda ta fi
sauran shanu kyawon ƙira da lafiya. Cikin shanun ƙasar Hausa kaf, gudale ta fi kyawon jiki da babbar hantsa mai
yawan madara. Ana yi mata kirari da, ‘Gudale karsanar shanu’. Idan kuwa aka ce
mutum karsani ne, to, ana nufin ya fi sauran jama’a kyawawan halaye da ma ƙirar jiki. Saboda haka salon kinaya da Haliru ya yi da Gudale,
yana nufin Alhaji Giɗaɗo Ibrahim Yabo. Ke nan a cikin
mutanen da Haliru ya sani, Giɗaɗo ne ya fi yawan kyawawan halaye
kuma mai kyawon halitta.
4.1.3 Bayanin
Diddigin Mawaƙi
An haifi Haliru Wurno
cikin shekarar 1925 a ƙauyen Ƙwargaba na ƙasar Wurno ta Jihar Sakkwato.
Abin lura a nan shi ne, Haliru Basakkwace ne kuma Bagiɗaɗe. Sarauta
ce ta kai kakansa a Wurno inda ya yi Sarkin Rima. Saboda haka Haliru
Wurno, mai iya zama Wazirin Sakkwato ne da ya kasance a raye har yanzu.
Haliru Wurno ya tashi cikin
zuri’ar da ilmi ne safararsu. Wato Giɗaɗawa, waɗanda suka
samo sunansu daga Usman Giɗaɗo ɗan Laima.
Shi kuwa Giɗaɗo shi ne wazirin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Shehu
Usmanu ɗan Fodiyo, Allah ya yi musu rahama, amin. Bagiɗaɗe ba ya
da wani abin tinƙaho da ya wuce ilmi da neman sa.
Saboda haka Haliru ya buɗe ido da neman sani. Ya yi karatu a gida da kuma makaranta kamar
sauran giɗaɗawa. Ya yi karatun allo da na sani a makarantar Liman Macciɗo a garin
Sakkwato. Manyan malamansa na karatun sani sun haɗa da
Liman Macciɗo da Malam Joɗi ɗan Waziri
Abdulƙadir Macciɗo da
Waziri Junaidu ɗan Waziri Muhammadu Buhari (ƙane ne ga
waziri Macciɗo), duk a Sakkwato. A Wurno kuwa akwai Malam Bayero da Malam
Abubakar Uban Lale. Haka kuma Haliru ya yi karatu a makarantun zamani na
lokacinsa. Tsakanin shekarar 1943 da 1947 ya yi makarantar da ake kira “Sokoto
Qadi School”. Malamansa a makarantar sun haɗa da
Waziri Junaidu da Malam Ahmadu Ɗan Hannun
Giwa.
Haliru yana sauka a wannan makaranta sai ya
zarce zuwa makarantar nazarin ilmin Sharia ta Kano, wato ‘Kano Law School’. Ya
shekara huɗu a can
inda ya kammala a 1951. Malamansa a wannan makaranta sun haɗa da Shaikh Awad Muhammad Ahmad
da Malam Nasiru da kuma Malam Abubakar Gumi. Haliru yana kammala wannan
makaranta sai aka ɗauke shi
aiki a matsayin malami mai karantar da ilmin addinin Musulunci da Larabci a
makarantar Maru wadda a lokacin ake kira Elementary Training Centre (E.T.C.)
Maru. To amma bayan shekara ɗaya da
wata shida sai aka ɗauke shi
aiki a ma’aikatar
shari’a ta
lardin Sakkwato. Ya yi aiki nan a matsayin akawun kotu tun daga 1952 har zuwa
1965, lokacin da ya bari ya koma ga karantarwarsa. Ya zauna a
makarantar Nizamiyya ta ‘Yar Akija a garin Sakkwato a matsayin malamin addini
da Larabci. A lokacin ne ya rubuta ‘Waƙar Fanda’ ko ‘Waƙar Danja’ wadda ta shahara a tsakankanin ‘yan makaranta a Sakkwato da kewaye. Shekara
biyu da ‘yan
watanni ya yi yana karantarwa a Nizamiyya kafin ma’aikatar shari’a ta neme shi da ya koma ya yi alƙalanci.
Ya karɓi wannan
gayyata ya kuma ci gaba da aikin har zuwa 1981 lokacin da ya bari don
ganin damarsa, ya sake komawa ga karantarwa.
A taƙaice dai
Alƙali Haliru Wurno, karantarwa da alƙalanci ne
ayyukan da ya yi. A sanadiyyarsu ya zauna garuruwa da dama a yankunan Sakkwato
da Zamfara da na Argungu.
A Sakkwato ne Allah
ya karɓi
ran Haliru cikin gidansa na Kwalejin Fasaha Da Larabci ta Abubakar Gumi,
ranar Alhamis 16 ga Oktoba na 2003 bayan sallar La’asar kuma kusan sallar
magariba. Allah ya gafarta masa dukan kurakuransa, ya saka masa da aljannar
Firdausi, amin.[i]
4.1.4Gudale: Gazal Na Waƙoƙin Hausa
An riga an yi bayani cewa
gazal ɗin da ya
fito cikin waƙar da ake kira ƙasida, shi ne zai riƙe sunan
gazal, a yayin da wanda aka samu mai cin gashin kansa a mazaunin waƙa shi ne a nan za a wa laƙabi da
gazaliya. To ita waƙar Gudale a wannan muƙala an ɗauke ta a
matsayin gazaliya, ko ma a ba ta suna, “Gudale”, saboda
la’akari da
yadda Hausawa ke son nagge gudale.
Za a iya raba waƙar zuwa kaso biyu kuma daidai wa daida. Kashi na ɗaya shi ne baiti na ɗaya zuwa na hamsin. Kashi na biyu
kuwa daga baiti na 51 zuwa na 100. Kaso na ɗaya ya ƙunshi raɗaɗin da mawaƙi ya ji saboda rashin mai kula da
shi, wanda zai ɗauki
nauyinsa da shi da lalurorinsa. Shi kuwa kaso na biyu ya ƙunshi daɗin da
mawaƙin ya ji saboda samun Giɗaɗo ya rungume shi, ya ɗauki kowane irin nauyinsa. Sharhin waƙar zai kasance a kan waɗannan ɓangarori
biyu.
4.1.4.1Raɗaɗin Rashin Masoyi
Alhaji Haliru Wurno
ya buɗe waƙar Gudale da irin baitocin da ake kira basmala, yana cewa:
1. Na yi kiran Allah shi ishe ni
Al’amarin ga da yad dame ni
2. Na yi salatu ga Hairil halƙi
Ahmada ya zo man da Mubini
3. Na yi salatu dubu da salama
Alaihi wa alihi ahlid dini
A baiti na ɗaya Haliru ya cika wata ƙa’idar waƙar da ake
kira ƙasida, wadda ta bukaci mawaƙi yin amfani da ‘amsa-amo
mai kiɗa’, wato inda amsa-amon ciki da na waje duk iri
ɗaya ne,
kuma hakan yana nuni da cewa wannan shi zai kasance amsa-amon waje a duk tsawon
waƙar. Ba mamaki saboda gazaliya waƙar da ta
samo ‘yanci ce
daga nasiib na
cikin waƙar ƙasiida
Abu na biyu da za a lura da shi a nan shi ne,
a ɗangon farko
na baiti na ɗaya, mawaƙin ya fara shigar da nau’in nasiib (nau’in
da ke ɗauke da
gazal). Roƙon da ya yi na Allah ya /ishe/
shi, manuniya ce ta irin raɗaɗi ko juyayin ciyon rashin masoyi
ko nisansa daga Haliru. Kalmar tana nuni da cewa mawaƙin ya matsu, bai da ƙarfi bale
ya fitar da kansa daga matsuwar. Yana roƙon Allah
da ya tabbatar da ɗorewar
soyayyar da ke tsakaninsa da masoyin da zai ambata cikin waƙar can gaba, masoyin da zai gabatar da salon kinaya, ya kira shi ‘Gudale’
Bayan Haliru ya gama yin wannan addu’a a
baiti na 4 sai ya faɗa mana
cewa ƙara ce yake gabatarwa domin ya
tabbata bai iyawa da annamimancin da ake yi masa don a raba shi da masoyinsa.
Ya yi haka ne a baiti na 5,
5. Na zaka ƙara na
kawo ta
Jalla gare ka ka dai dube ni
To amma bai kawo cikon wannan tunani ba sai a
baiti na 65 da na 66, inda ya yi amfani da ‘salon hira’[i] ya cusa cikon tunanin da ya kawo a
baiti na 5 ɗin ga
bakin ɗalibansa,
65. Nasiru ya ce Baba ka duba
Ba a yi ma wani takin reni
66. Na san dauri kana makaranta
Gulma akai maka don ka yi muni[i]
A tsakanin waɗannan baitocin ne Haliru ya shiga tumƙar jigon soyayyar da ke tsakaninsa da shugaban makarantarsa, ta
hanyar kawo sunayen waɗanda ya
tafi wurinsu don su rungume shi. To amma duk wanda ya nufa ko dai ya kore shi
ko ma ya nufi cuta masa.
Mai karatu ko saurare ba zai yi saurin lura
da wannan tumƙa ba sai ya kai inda mawaƙin ya ambaci ‘gudalensa’ a can da nisa. Dalilin haka kuwa shi ne,
Haliru ya yi amfani da salon ‘laƙabi’, inda
mawaƙi kan tsara magana ta amfani da
wasu abubuwa musamman dabbobi domin ya ɓoye haƙiƙanin
manufarsa, ko kuma dangane da wasu mutane da bai son ya bayyana sunayensu. A
wannan waƙar, ta amfani da salon ‘shillo’[i] Haliru
ya bayyana yadda ya sha sheƙawa zuwa
ga wasu dabbobi (mutanen da ya sani) domin ya samu agajinsu, ya ji sanyi saboda
rashin da yake hange ya same shi (gulmar da yake ganin an sa tsakaninsa da
masoyinsa), amma duk a banza. Ba dabbar (mutumin) da ta tausaya masa. Da farko,
lokacin da Haliru ya ga haɗarin da yake
ciki:
6. Na ga rashin abkin kayana
Don haka tsoro ya ribce ni
7. Na ga dare da subahin haske
Ga kuma rana ta dushe ni
8. Na yi farat na sheƙa inwa
Na ga kwamarci ya kore ni
Wannan tsoro da ya kama shi ya sa Haliru ya
ruɗe har ya
rasa inda zai yi:
9. Na ga ruwan gulbi na zallo
Na zo na shiga sun toye ni
10 Na tuma na koma can ganga
Ba wani mai jinya ya fake ni
A nan laƙabin
ruwan gulbi watakila yana nufin wani mutum ko wasu mutane da mawaƙin ya sani kuma yake hangen suna da hali da zarafin su rungume
shi. To amma lokacin da ya je gun su sai ya tarar da (watakila) su ne suke
neman raba shi da masoyinsa. Ruwan gulbi ne masu zafi da ƙuna. Saboda haka ne mawaƙin ya bar
waɗannan
mutane don ya sake shawara, duk kuwa da cewa yana cikin jin raɗaɗin abin da suka ƙara yi
masa na cuta. A ƙarshe dai sai ya zaɓi ya je wurin waɗanda ya san masu hali ne don ya
zama bara gare su. Wato dai ya kwaikwayi tsuntsuwar nan balbela wadda ke bin
shanu don ta yi kiyo. Duk lokacin da tafiyar shanu ta tayar da fari sai balbela
ta bi su ta kama. Sai ta samu abinci albarkar shanu. Haka Haliru ya zaɓi ya yi, albarkar masu hali ya
samu nasa abinci.
Haliru ya nufi giwa amma sai ta zabura ta sheƙa da gudu ta bar shi. Sai Haliru ya nufi karkanda wanda nan take
ya kore shi. Ya wuce zuwa gidan zaki sai ya tarar ba ya nan. Zaki a tunanin
Hausawa sarki ne. Sarki kuwa mai ceton talakawa ne, mai taimakon mara ƙarfi ne. Saboda haka da mawaƙin ya ce
zaki /bai nan/, watakila yana nufin ya je ne wurin wani mai riƙe da wani babban muƙami don
ya taimake shi sai shi mawaƙin ya
kasa samun ganin wannan mai muƙami bale
ya taimaka masa.
Haka dai Haliru ya riƙa kai koke inda dabbobi (mutane) dabam daban waɗanda suke da irin nasu halin, don
su taimaka masa. Kama daga masu iko zuwa ga masu ƙarfin yi,
da waɗanda kome
ba su iya taɓukawa,
har zuwa ga waɗanda ta
kansu kurum suke iya yi, da kuma masu biɗar wanda za su cuta:
24. Na ga barewa na tambai ta
Inda gada take don ta riƙe ni
25. Na ce mat ta gwada mini hanya
Inda gadar take ko ta rake ni
26. Na ga gada da gudu ta sheƙo
Tac ce min tafi kar ka biyo ni
27 Na ga gudun da takai na ɓakita
Na jaye mata ta hauro ni
28 Na yi ga zomo bawan Allah
In shiga kurhinai ya fake ni
29 Na san zomo bai da mugunta
Ko da gashin kansa ya ba ni
30 Na ishe kurhinai sai kashi
Na ga kare yad dunfaro ni
31 Na riƙe sandata
damana
Kalbu iso in ɗebe reni
32 Na yi farat in mangare aura
Kuba faƙyau yab
bar ni anini
33 Na ga dila da biri ga kura
Zaki na kusa yah haure ni
34 Na ce gawa ukku kuna nan
Ba ni zama ƙura ta bito ni
Kai har ma da masu ilmin addini waɗanda Haliru yake ganin cewa ƙarfin imanin da suke da, shi zai sa su taimaka masa. Haliru bai da
abin da zai yi illa ya yi gaba! To amma duniya ta canza:
35 Na yi gabas wajjen yanyawa
Kila dibaratai ta ishe ni
36 Na ishe limami yanyawa
Ga ni mu’allimu zo ka daɗe ni
37 Na ga ashe shi ma tai zahi
Sa’alabu ya ce tashi ka bar ni
38 Na yi zugum ya ce kai tashi
Ba ka ganin inwa ta bar ni
39 Na yi zufa rana ga zafi
Matata ita ma ta bar ni
40 Na ce Mallam ka san Allah
Yac ce min ai shi yay yo ni
41 Na ce dubi hadisin tanyo
Ba ka yi min girman addini
42 Na ga kamar maganar ta kammai
Sa’alabu ya ce kai ka fi ni
43 Na ga kana iya kanka da kawo
Kwanana huɗu ban da sukuni
44 Na yi biɗar ƙannen matata
‘Ya’yana huɗu dut sun bar ni
45 Na ce assha na sa ƙaimi
Kar ya tumam mini ko ya buge ni
A waɗannan baitoci ya yi amfani da salon laƙabi domin ya ƙirƙiro salon ‘yanka’. Wato ya yi kakkausar suka ga masu ilmi a
wannan zamani. Baitocin suna nuni ne da cewa za ka ga muitum ya tara ilmi, yana
sane da kowane umurnin Allah da Manzonsa kan yin taimako ga mabukata, amma kuma
su ne kan gaba a bahilci, kamar yadda ’limami yanyawa’ ya yi da Haliru! Duk da
girmamawar da Haliru ya ba shi, ya ce, /Ga ni mu’allimu zo ka daɗe ni/, mu’allimun kuma ‘limami’ ɗin bai ji nauyin korar Haliru ba.
Hausawa sun ce, babu maraye sai raggo. Haliru
ya ci gaba da neman wanda zai iya tausaya masa har dai Allah ya amshi roƙonsa, ya kai shi inda garken shanu. A cikin shanun ne ya samu jin
sanyi kuma ɗayansu ta
karɓe shi
hannu bibbiyu, ya shiga daula:
46 Na fita na yi gudu bisa dutsi
Na ishe shanu sun tarbe ni
47 Na ce shanu to don Allah
Na zaka gun ku ku dai cece ni
48 Na ga farar ‘yan nagge gabana
Ga ta fara sai tan nuno ni
49 Na ga ta tunan shi taka niyya
Na ja baya ƙafa tai duni
50 Na sheƙa ga
gijen hankaka
Nij ji kiran baƙara ta biyo ni
51 Na koma ma gudale ga shanu
Mai hantsa cike ta karɓe ni
A nan ne mawaƙin ya
canza rawa, daga nuna ƙauna a kaikaice zuwa ga wanda
yake wa waƙar, ya fito sarari ya bayyana wa
masu saurare ko karatun waƙarsa
wanda yake ƙauna yake kuma yabo. Ya kuwa
gabatar da wannan bayani ne ta amfani da ‘salon hira’
tsakaninsa da ɗalibansa:
52 Na yo zane yara ku gane
Wagga gudale da taƙ ƙwasshe ni
53 Na san ɗana kila Basiru
Zai iya ganewa ya rige ni
54 Nasiru ya ce na san naggen
Ɗan Ibrahi
na mai auni
55 Alhaji na kuma babban zaure
Babu irinai bai son reni
56 Alhaji wanga Giɗaɗo tsayayye
Shugaba na mai son addini
Haka Haliru ya ci gaba da nuna ƙauna da yin yabo ga wannan ‘gudale’ (Giɗaɗo Ibrahim) har zuwa ƙarshen waƙar. Ya tabbatar ma ɗalibansa da cewar da suka yi ai ‘gudale’ da ya ambata ba kowa ba
ne face Giɗaɗo, shugaban makaranta. Tsananin ƙaunarsa ga wannan Gudale ta kai ƙoli don
kuwa Haliru ya ce,
70 Na ce yara ɗiya kun gane
Giɗaɗo
Faransafa yai ihsani
71 Na saki al’amarinsa gaba ɗai
Ba ni da ja to mit tiƙo ni
72 Na yi biya na ba da amana
Ban ga mutum ba da yaɗ ɗauke ni
73 Na san ba a yi mai fadanci
Ya san Allah kowane fanni
Waƙar yabo
ga masoyi ba ta rabuwa da zambo da zolaya. A kan haka ne Haliru ya soki ‘yan
adawa waɗanda su
ne watakila yake ganin su ne masu yi masa ƙullin
sharri ga shugabansa kuma masoyinsa:
74 Na ga ƙudara da
bai son hairi
Ya game huskatai ya bar ni
75 Na ga maƙarhu ɗan mazari ko
Ya yi ɗuminai ya soke ni
76 Na ga ƙudan
tsando ya cizan
Sai bararoji da yaz zole ni
77 Na manguwa ɗan zomo ya shura
Wancan durwa baƙi ya ƙi ni
78 Noƙe da kai ƙarya yaka kaya
` Sai ƙazafi da ƙire yai shaini
79 Na gane ma macijin ƙaiƙai
Ban da sane sai yac cije ni
80 Na ga zaman ga ga yau na shirya
Ba ni bari kuturu ya buge ni
A waɗannan baitoci Haliru ya yi kusa da ya ambaci sunayen waɗanda yake yi wa zambo. To amma
sai ya yi amfani da salon kinaya ya yi habaici. Ta haka da su ɗalibansa, da mallaman cikin makarantar
da kuma shi kansa masoyin Haliru, duk za su iya su gane ko da wa yake. Dukansu
suna iya gane mutanen domin suna zaune tare da su cikin makaranta kuma sun san
su. A can baya mun ji wani ɗalibin
Haliru yana cewa:
65. Nasiru ya ce Baba ka duba
Ba a yi ma wani takin reni
66. Na san dauri kana makaranta
Gulma akai maka don ka yi muni
A ƙarshe,
Haliru ya rufe waƙarsa kamar yadda waƙoɗin gazal
da na ƙasida na Larabci kan rufe. Wato a
baitin ƙarshe na gazal ko ƙasida mawaƙI kan faɗI sunansa amma a kaikaice. Shi
Haliru har da ƙarin cewa kowane mutum ya san
shi, ba sai ya fito ɓaro-ɓaro ba. Ga yadda ya sakaya sunan
nasa:
100. Na gama waƙata Alƙali
Alhaji Wurno mutum ya san ni
KAMMALAWA
Wannan muƙala ta yi
ƙoƙarin ta bi diddigin tushen waƙar da ake kira ghazal. Ta
bayyana cewa irin wannan waƙa ta
Larabawa ce, su suka ƙirƙiro ta
tun zamani mai tsawo, kafin zuwan Musulunci. Muƙalar ta
nuna cewa a can farko ghazal wani ɗan gutsure ne cikin wata sigar waƙar da ake kira ƙasiidah. To amma
bayan Musulunci ya bayyana, ilmi ya bunƙasa,
albarkar Alƙurni da Hadissan Manzo (s.a.w),
sai wannan gutsure na ghazal ya
bunƙasa, ya samu ‘yanci
daga ƙasiidah musamman
cikin ƙarni na bakwai (ƙ.7) da na (ƙ.8). Tun daga wannan zamani ghazal ya
ci gaba da yaɗuwa a duk
faɗin duniya
cikin adubba dabam daban.
A ƙasar
Hausa kuwa wannan nau’in waƙa ya samu karɓuwa ga
malamai musamman na ƙarni na goma sha takwas da na sha
tara (ƙ.18/19). To amma waɗannan malamai, cikinsu har da
Shehu Usmanu ɗan Fodiyo
da ‘ya’yansa, Muhammadu Bello da Muhammadu Buhari,
da kuma ƙanensa Mallam Abdullahi, dukansu
cikin harshen Larabci suka rubuta ghazal. Sai a ƙarni na
20 zuwa yau, ƙarni na 21, aka fara samun gazal
cikin harshen Hausa. Hana-rantsuwa ita ce waƙar
Lisanul Hali da ta zo a ƙarshen ƙarni na 19.
Muƙalar ta
kawo shawarar rarrabewa tsakanin gazal ta cikin ƙasida da
gazal mai ‘yanci.
Gazal ta cikin ƙasida ta tsaya da sunan na asali.
Gazal kuwa mai cin gashin kanta a kira ta ‘gazaliya’ ko
‘gudale’, wato ta amshi sunan waƙar Haliru
Wurno.
Abu ne mai amfani a nazarin waƙoƙin Hausa a yi waiwaye zuwa ga
rubutattun waƙoƙin ƙarni na 18/19, da kuma na marubuta waƙoƙin Hausa na ƙarni na 20, musamman waɗanda suka taso da ilmin addini Musulunci tun ƙuruciyarsu har suka girma. A waiwayen nan, manazarta su nazarci waƙoƙin waɗannan marubuta ta fuskar tasirin
da rubutattun waƙoƙin
Larabci suka yi a kan nasu waƙoƙi. Ta haka ne za a iya zaƙulo wasu
abubuwa da ba a lura da su ba can baya. Waƙar gazal
ta je al’ummomi da yawa ta shiga cikin adubbansu, ta yi zaune dangalgal. Ta
shiga cikin adabin Hausa, kuma ga dukan alamu za ta yunƙura ta yi yadda ta saba. Ta hanyar yin aro mai kyau, mai amfani ne
adabin kowace al’umma kan
bunƙasa, ya inganta.
MANAZARTA
Abdulƙadir, Ɗ. (1978) The
Poetry, Life and Opinions of Sa’adu Zungur, Zaria:
NNPC.
Ainu, A.A. (2007), ‘Rubutattun Waƙoƙin Addu’a Na
Hausa:Nazarin Jigoginsu Da Salailansu’, kundin dfigirin Ph.D., Sakkwato:Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Birnin Tudu, S.Y. (2002), Jigo da Salon Rubutattun Waƙoƙin Furu’a na Ƙarni na
Ashirin’ kundin
digirin Ph.D., Sakkwato: Jami’ar Usmanu
Ɗanfodiyo.
Ɗan Fodiyo, A (1383 H.), Tazyin al-Waraƙaat, Mallam Abdullahi ɗan Fodiyo ya rubuta wannan
littafi cikin shekarar Hijira ta 1228 H. (1813/14 Miladiyya).
Ɗangambo, A. (1980), “Hausa Wa’azi verse
from C.A. 1800-C.A. 1970. A Critical Study of Form, Content, Language And Style”, kundin Ph.D, Jami’ar London.
Ɗangambo, A. (2007), Ɗaurayar
Gadon Feɗe Waƙa (sabon tsari), Zaria: amana publishers ltd.
ƊUNƊAYE: Journal of Hausa Studies 1-5, Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
(2004-20-14), Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Haɗeja, M.
(1980), Waƙoƙin Mu’azu Haɗeja, Zaria: NNPC.
Hiskett, M. (1975), A History of Hausa Islamic Verse, London.
Junaidu, S.W. (1985), “The Sakkwato Legacy of Arabic Scholarship
in Verse Between 1800-1890”, kundin digiri na Ph.D., London: University of
London.
Malumfashi, I.M. (2009), Adabin Abubakar Iman, Kaduna:
Fisbas Media.
Malumfashi, I.M. (2002), “Ƙagaggun
Labaran Hausa: Abin da Muka Sani da Wanda ba Mu Sani ba Ta Fuskar Tarihin
Adabi”, takardar da aka gabatar a taron ƙara wa
juna sani, Sakkwato: Jami’ar Usmanu
Ɗanfodiyo.
Sa’id, B. (1987), Dausayin Soyayya,. Zariya: Gaskiya.
Yahaya, I.Y. (2008), Hausa a Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce
Cikin Hausa, Zaria: NNPC.
Yahya, A.B. (1987), “Hausa Verse Category of Madahu with Special
Reference to Theme Style and Background of Islamic Sources and Belief, kundin
Ph.D., Jami’ar, Sakkwato.
Yahya, A.B. (2001), Salo Asirin Waƙa, Kaduna:
Fisbas Media.
Yahya, A.B. (2003)“Rubutattun Waƙoƙin Nasiha: Wani Ɓangare Ko
Kuwa Sauyin Salo A Cikin Rubutattun Waƙoƙin Hausa Na Wa’azi?”, cikin ALGAITA Journal of Current Research in Hausa Studies vol 1, No 3, Sashen
Koyar Da Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.
Yahya, A.B. (2004), ’Tsattsafin Raha Cikin Waƙoƙin Alƙali Alhaji Haliru Wurno’, cikin ZAUREN WAƘA:Mujallar Nazarin Waƙoƙin Hausa 1 (2013), Sakkwato: Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Yahya, A.B. (2012), ‘Tsattsafi: Wani Ɗigo Cikin Gulbin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa’, cikin ƊUNƊAYE:Journal of Hausa Studies 5, (2013), Sakkwato: Sashen Koyar Da
Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo
Yahya, A.B. da Idris, Y. (2014), ‘Gyara Ko Ɓanna: Gurɓata Waƙar Arewa Jumhuriya Ko Mulukiya’, muƙalar da
aka gabatar a Taron Yamai (Jumhuriyar Nijar) domin Tuna da Karrama Marigayi
Farfesa Muhammadu Hambali Jinju.
Yakubu, A.M. (1999), SA’ADU ZUNGUR: An Anthology of the
Social and Political Writings of a Nigerian Nationalist, Kaduna:
Nigerian Defence Academy Press.
ZAUREN WAƘA:
Mujallar Nazarin Waƙoƙin Hausa 1, Sashen
Koyar Da Harsunan Nijeriya (2013), Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
https://www.wordnik.com/words/ghazal: to
display love to the loved one via speech; to exchange talk of love with the
loved one, 05/04/2014, 02.03 a.m.
http://en.wikipedia.org/wiki/Ghazal,
05/04/2014, 02.45 a.m.
www.ghazalpage.net/prose/notes/short Jalajel,
D. (2007).
- Waƙoƙin Alƙali Alhaji Haliru Wurno da marubucin wannan muƙala ya mallaka.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.