Ticker

6/recent/ticker-posts

Yanda Ake Dafa Indomie Ta Yi Daɗi

Kayan haɗi

  • MANGYADA
  • ATTARUGU
  • TATTASAI
  • TOMATOES
  • INDOMIE
  • KWAI DAYA.

DA FARKO KI JAJJAGA ATTARUGU DA TATTASAI DA ALBASA DAIDAI DA TAFARNUWA.

KI DORA TUKUNYARKI A WUTA, KI SAKA MAI DAIDAI IDAN YA YI ZAFI, KI SAKA TOMATOES GUDA BIYU DA KIKA YANKA SU KANANA, KI SAKA JAJJAGEN KAYAN MIYARKI, KI GAURAYA, KI SAKA MAGGIN CIKIN INDOMIE DAYA, DA CURRY DA KAYAN KAMSHI IDAN KINA SO DAIDAI, ZA KI IYA SAKA MAGI IDAN BAI YI DAIDAI BA KADAN.

KI GAURAYA SOSAI KI TABBATAR KOMAI YA YI DAIDAI YA SOYU YA KAMA JIKINSA BABU RUWA KO KADAN A CIKI, SAI KI FASA KWAI KI ZUBA A KAI KI GAURAYA, IDAN YA SOYU GABA DAYA SAI KI SAUKE.

KI DORA RUWA A WUTA IDAN YA TAFASA, KI KAWO INDOMIE YADDA ZAI ISHE KI, KI ZUBA KI DAFA DAIDAI DAHUWAR YA YI KYAU.

SAI KI SAUKE, KI SA A SHATA YA TACE, SHKN KI ZUBA A FLAT KI SAKA WANNAN SOURCE DIN A SAMA, SAI A CI LAFIYA😋.

Post a Comment

0 Comments