Ticker

6/recent/ticker-posts

Marar Lafiya Ana Ɗauke Mishi Azumi Ne Har Sai Ya Warke Ya Rama

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Allah ya Kara ma malam ililmi da basira. Ana bi na azumi(20) sabida ban Sami daman ramawa sabida ciwo Kuma bana iya ciyarwa sabida iyayena ba suda Hali. Mm ya zan yi yanzu?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

Bawan Allah wace amsa kake so a baka? Ka zo da zantuka da ke nuni zuwa ga amsar da kake so a baka, ka karanta mani ita a baki ne kaɗai ya rage baka yi ba.

Kafin na baka amsa ga tambaya, kana nufin watanni goma sha ɗaya da suka wuce, dukan su, kana kwance baka lafiya ne?

Na biyu: wa ya ce da kai, maras lafiya zai ciyar ne?

Bayan haka waye ya baka fatawar iyayen ka ne za su ɗauki nauyin ciyarwar da ke kan ka, ballantana ka fara gabatar da uzurin talaucin su.

Kana nufin yanzu haka maganar da muke, kwance kake baka da lafiya?

Ƙa'ida ita ce, duk maras lafiya, Allah ya ɗauke mashi azumi, har sai lokacin da ya warke. Idan kuma har ya mutu bai warke ba, babu laifi a kan sa, kamar yadda babu ramako a kan shi ko a kan waliyyan sa.

Don haka za ka zauna har zuwa lokacin da Allah ya baka lafiya, sannan ka rama azumi ashirin da ka sha a sanadiyyar waccan rashin lafiyar, wannan shi ne a kan ka.

Allah ya ce da maras lafiya da matafiyi, su rama azumi bayan ya warke daga ciwon shi, matafiyi kuma a lokacin da ya dawo gida

(.. وَمَن كَانَ مَرِیضًا أَوۡ عَلَىٰ سَفَرࣲ فَعِدَّةࣱ مِّنۡ أَیَّامٍ أُخَرَۗ یُرِیدُ ٱللَّهُ بِكُمُ ٱلۡیُسۡرَ وَلَا یُرِیدُ بِكُمُ ٱلۡعُسۡرَ..... )

[Surah Al-Baƙarah 185]

Wallahu ta'aala a'lam.

 Amsawa:

 Malam Aliyu Abubakar Masanawa

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GhLY39kRlZEIdcZUmGchEm

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments