KAYAN HADI:-
- NAMA
- WAKE
- KWAI
- ATTARUGU
- ALBASA
- MAGGI DA GISHIRI
- MAN GYADA
KI WANKE WAKENKI KI ZUBA ATTARUGU DA ALBASA, KI KAI A MARKADA MIKI DA
KAURI.
KI BUGA SOSAI BAYAN AN MARKADA, KI DAKA NAMA KI ZUBA, KI FASA KWAI KI ZUBA,
KI SAKE BUGAWA SOSAI, KI SAKA GISHIRI DA MAGGI DA CURRY, KI DINGA BUGAWA.
IDAN KIN KAMMALA, DA MA MANKI (MANGYADA) YA YI ZAFI, SAI KI DINGA SAKAWA A
MAI MAI ZAFIN KINA SOYAWA.
IDAN YA YI JA YA SOYU, SAI KI KWASHE, KIN KAMMALA HADA KOSAN NAMA😋
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.