Ticker

6/recent/ticker-posts

Giya Da Turare

Giya ba najasa bace, duk da cewa ƙazanta ce, kuma shanta yana daga cikin manya-manyan zunubai, sai dai babu wani dalili da ya nuna cewa najasa ce.

 ALLAH TA'ALAH ya ce:

Yaku waɗanda suka yi imani ku sani cewa lallai giya da caca da gumaka da rantsuwa da kibau ƙazanta ne daga aikin Shaiɗan don haka ku nisance su ko kun rabauta.

[Al-ma'ida :90]

Abin da ake nufi da ƙazanta a nan shi ne ƙazantar ɓoye ba ta fili ba, kamar yadda caca

da gumaka suke ƙazanta amma ba ta zahiri ba.

 Da wannan ne za mu gane halaccin amfani da turaren da suke da alkahol a cikinsu, saboda shi Alkahol ana samun shi ne daga giya.

 Inda giya za ta zuba a jikin tufafin wani alhali yana da alwala, to wannan giyar ba za tasa kayansa su zama baza su yi sallah ba, domin ita ba najasa bace, ƙazanta ce, shanta haramun ne.

 

 Kaso 95 daga cikin turaren fesawa akwai jiya a cikinsu, kuma fesasu ba haramun ba ne, kuma baya hanawa a yi sallah a cikin tufafin.

ALLAH shi ne mafi sani.

Duk mai neman ƙarin bayani ya yi mana magana ta private.

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments