Ticker

6/recent/ticker-posts

Ya Yi Buɗa Baki Da Jima'i Da Matarsa?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Aslaam alaykum mlm barka da warhaka dafatar kana lapia. malam minene hukuncin Wanda ya yi azumi amma bai yi buɗa baki ba, ma'ana bai sha ruwa bayan ladan ya kira sallah. Sai ya yi jima'i da matarsa, Ya azuminsa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, Azuminsa ya yi daidai, mutukar ya sadu da ita ne bayan rana ta fadi.

Annabi ya yi umarni ayi buɗa baki da dabino ga wanda ya samu dama, in ba hali kuma ayi da ruwa kamar yadda ya tabbata a hadisai.

Abin da ya gabata yana nuna cewa: Yin buɗa baki da dabino ko ruwa shi ne sunna, saidai wanda ya fara da jima'i azuminsa ya inganta, tun da Allah ya halatta masa jima'i a daidai wannan lokacin kamar yadda aya ta: 187 a suratul Bakara ta nuna hakan.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:- Dr. Jamilu Zarewa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BpO6i5KwGBm8IcVtlhBr0j

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments