Hanyoyin Tsarkaka Daga Najasa

    Tsarkin Ƙasa Mai Najasa

    Idan najasa ta samu ƙasa, to wannan najasa tana gushewa ne da ruwa ko waninsa, saboda hadisin mutumin ƙauyen-nan da ya yi fitsari a masallaci,

     Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce:

     Ku ƙyale shi, ku kwarara ruwa guga ɗaya a kan fitsarinsa, ko ku zuba guga babba ta ruwa.

    [Bukhari da Muslim].

     Ita kuwa najasar da take daga ruwa, tana bushewa, to ta tsarkaka, saboda hadisin Abu Ƙilaba (R.A) ya ce: Idan ƙasa ta bushe, to ta tsarkaka.

    [Bukhari ne ya rawaito shi].

     TSARKAKEWAR RUWA MAI NAJASA

    Yana tsarkakuwa idan aka haɗa shi da wani ruwan mai yawan da zai gusar da alamar najasar, kamar yadda yana tsarkakuwa idan aka tace da na’urorin zamani da ake tace ruwa da su.

     Tsarkake Tufafi Mai Najasa

    Ana wanke ta da ruwa, a kankare, a matse, har najasar ta gushe.

     TSARKAKE SHINFIƊA

    Ana wankewa da ruwa, ko kuma da abubuwan tsaftacewa na zamani, kuma a kankare, har najasar ta gushe.

     TSARKAKE FATAR MUSHE

    Fatar mushen Dabbar da ake cin namanta ana tsarkake ta da jima, saboda faɗin;

    Manzon ALLAH {s.a.w} Idan aka jeme fata, to ta tsarkaka.

    [Muslim ne ya rawaito shi].

     Jima ita ce, sanyawa fata wasu sina darai waɗanda za su sa ta yi laushi, ta daina wari.

     Idan kuwa dabbar da ake ci ba mushe ta yi ba, yanka ta aka yi ta hanyar da shari'a ta amince, to fatarta mai tsarki ce.

     FATAR MUSHEN DA BA A CIN NAMANTA

    Fatar wannan dabbar tana ɗaukar hukuncin mushe, ba ta tsarkaka, ko da an yanka dabbar ta hanyar shari'a

    Tsarkake Fitsarin Yarinya Da Fitsarin Yaron Da Basu Fara Cin Abinci Ba

    Ana wanke fitsarin yarinya ko da jaririya ce, amma fitsarin yaro ana yayyafa ruwa ne kawai, saboda faɗin:

    Manzon ALLAH {s.a.w} Ana wanke fitsarin yarinya, ana yayyafa ruwa ne a fitsarin yaro.

    [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

     Ita kuwa rigar da fitsari ko maziyyi ko wadiyyi, ya taɓa sai kawai a yayyafa ruwa a wurin da maziyyin ko wadiyyin ya taɓa.

     Saboda hadisin Sahli Ɗan Hunaif (R.A), ya tambayi Annabi {s.a.w} ya ce:

    Nace ya Manzon ALLAH {s.a.w} yaya zan yi da abin da ya taɓa tufata na maziyyi da wadiyyi, sai ya ce:

     Ya isa ka ɗebi tafi ɗaya na ruwa ka yayyafa wa tufafinka, inda kake ganin ya taba.

    [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

    TSARKAKAR DOGUWAR RIGAR MATA

    Idan wani abu na najasa ya maƙale a cikin rigar mace, tafiyar da take a wuri mai tsarki yana isar mata, ƙasa tana tsarkake ta, saboda faɗinsa: Abin zai biyo bayansa yana tsarkake shi.

    [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

    TSARKAKAR ABINCIN DA YAKE DASKARARRE

    Ana tsarkake shi ta hanyar ɗebe najasar da inda ta taɓa a zubar da ita, abin da ya rage yana nan da

    tsarkinsa, saboda abin da ya tabbata daga Manzon ALLAH {s.a.w} An tambaye shi a kan ɓera idan ya faɗa kakide,

     

    Sai ya ce:

     

    Ku jefar da ɓeran da gefen wurin da ya taɓa, ku ci saura man naku.

     

    [Bukhari ne ya rawaito shi].

     

    TSARKAKE ABUBUWA MASU ƘYALLI KAMAR MADUBI DA KWALBA

    Ana gogewa ne har alamun najasar su gushe.

     YANA DA KYAU MU SAN WANNAN

    • A ƙaida duk wani abu mai tsarki ne, sai idan dalili na shari'ah ya nuna najasa ne.

    • Idan najasa ta faɗa a kan wani abu, aka kasa gane inda ta faɗa, to sai a wanke abun gaba ɗaya.

    • Idan najasa ta zama wani abu daban, kamar a ƙona kashin jaki ya zama toka, to ya zama mai tsarki.

    ALLAH shi ne mafi sani.

    ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu.

    Duk mai neman ƙarin bayani a yi mana magana ta private.

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    1 comment:

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.