Ticker

6/recent/ticker-posts

Ya Yi Bakance Ya Kasa Cikawa. Yaya Zai Yi?

Farko dai shi bakance makaruhi ne, a wani ɓangaren kuma haramun ne a wajan wasumalaman, saboda Annabi {s.a.w} yana cewa:

 Bakance bayazuwa da alkairi, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 1639. Sai dai ya wajaba a cika bakance idan aka yi.

 Wasu daga cikin malaman hadisi sun tafi a kan cewa idanmutum ya yi bakance ya kasa cikawa zai iya-yin kaffararrantsuwa,

 Saboda hadisin da aka rawaito daga Muslim alamba ta:1645. a sahihinsa, wanda Annabi {s.a.w} yake cewa:

 Kaffarar bakance irin kaffarar rantsuwa ce.

Duba Alminhaajna Nawawy 4/269.

 Saboda haka a bisa abin da ya gaba ta mutum zsi iya-yin kaffarar rantsuwa wato:

 Ya ciyar da miskinai goma, idan baida halin haka to, ya tufatar da su, idan baida halin haka, to ya 'yantakuyanga (baiwa),

 Idan babu hali, sai a yi azumi uku, kamar yadda ya zo a suratul Ma'idah ayata: 89.

ALLAH shi ne mafi sani.

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments