Ticker

6/recent/ticker-posts

Mutum Ne Yake Yin Kuskure Sallah Bai Sani Ba Sai Yanzu, Shin Ya Matsayin Sallolinsa Na Baya?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam Allah Ubangiji ya kara ɗauka da sani malam ina da tambaya, kamar yanzu mutum ne yake kuskure wurin yin sallah bai sani ba sai aka zo wata rana ya ji ana wa'azi a kan abun yagano yana kuskure wurin shin malam ya sallolinshi na baya suke kuma kamar farillace yake bari.

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa Alaikis Salaam:- Sallar Ki ta yi Babu komai a Kansa. Sai dai Kawai ki Tsaya Dakyau ki gyara ibadar Ki na gaba yanzu ne idan Kin yi Kuskure tun da kin Sani hukuncin zai hau kanki.

Sabida An yi Irin Wannan a Zamanin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihin Wassalam a Gaban Annabi, a Lokacin da wani ya zo Masallaci a gaban Manzon Allah ya yi Sallah ya idar, Sai Annabi ya ce masa koma ka yi Sallah domin baka yi Sallah ba, ya koma ya sake yin wani Sallar, Annabi ya sake ce masa ya koma ya sake yin wani domin ba ka yi Sallah ba, mutumin ya yi Sallah a haka har sau uku, ƙarshe mutumin ya ce ma Annabi shi iya yadda ya iya ke nan kuma kullum haka yake yin kayan sa, ya ce ba zai iya yin wanda ta fi shi ba, Sai mutumin ya ce ma Annabi koyamin yadda ake yin Sallah sai Annabi ya koya masa.

Lura da Cewa tun da Can wannan Mutumin duk Sallolinsa a Cikin Kuskure yake yin su, yanzu ne Annabi ya koya masa, amma Annabi bai ce Masa toh waɗanda ya yi a baya a Cikin Kuskuren nan ya biya su ko ya sake gyara su ba.

Annabi ba ce mai komai ba kawai ya koya masa yadda ake yin Sallah ne kawai ba tare da Annabi ya ce masa ka je ka sake na baya ba. Don Haka ita ma Sallar ta ya yi ba za ta sake su ba ko gyara su ba, Sai dai ta kiyaye gaba tun da yanzu ta ji, sannan ta yawaita yin Istigifari da Yin Nafiloli domin ya maye Waɗancan. Amma dai babu komai a Kanta Duk na bayan Sun yi ba za ta gyara ko ta sake yin wasu sabbi ba, sai dai ta kiyaye gaba. Dafatan Kin gane Koh?

WALLAHU A'ALAM.

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments