Sheikh Ibnu Uthaimin yana cewa: Huda Hanci zai iya zama canza halittar ALLAH, amma idan garin da matar data huda hancin take ana yın ado ahanci, ta yadda hakan ya zama al'ada, to babu laifi ayihakan.
Duba: Majmu'u Fatawa Ibnu Uthaimin 11/137.
Sheikh Abdul
Muhsin Al'abbad ya ce adarasinsa da yake gabatarwa a Harami, sai ya ce babu
laifiakan haka.
Bisa abin da ya
gaba ta ya halatta matar BAHAUSHE ta hudahancinta saboda ta sanya abin kwalliya
tun da al'adarsu ce,
Saboda ya tabbata
a zamanin sahabban Annabi {s.a.w} mata suna hudakunnansu suna sanya 'yan kunnaye kamar yadda
hadisin
Bukhari mai lamba: 98 yake nuni zuwa hakan.
ALLAH ne mafi sani.
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
Post your comment or ask a question.