Ticker

6/recent/ticker-posts

Wainar Fulawa

Wannan na ɗaya daga cikin jerin waƙoƙin Malam Khalid Imam da a kullum suke faɗakarwa da ilimantarwa da nishaɗantarwa. Yana taɓo fannoni daban-daban a cikin waƙoƙinsa, ciki har da abubuwan da suka shafi lamuran yau da kullum.

Mata ni zan bayani,

Gaskiya na baje a faifai,

Juyin wainar fulawa,

Matar da tà sami fuska,

Gangara da lagon mijinta, 

Ta ke yi mas a sauƙi.


Bai da fus a cikin gidansa,

Sai yadda ta so ta tsara,

Shi Salame yana ta bin ta,

Zungwi-zungwi a baya,

Ba ya iya yin kataɓus,

Ka ji mai hali na toro.


Ba ƙauna babu tausai,

Kasan wainar fulawa,

Juyata ake da ƙarfi,

Cikinta a kankaro shi,

Fuska a buga a kasko,

Ba a damu ba har ta ƙone.


Mace mai yi wa mijinta,

Suyar wainar fulawa,

Mace ce mai son husuma,

Ba ta son kowa a dangi,

Ta gan shi jikin mijinta,

Ka ji labarin su karya.


Mai ɗan tausai a mata,

Ita ce mai wa mijinta,

Juyin waina a tanda,

Ta shimkafa da sannu,

Ko tai sakaci ta kama,

Da sannu take cire ta 


Wasu matan ko a zahir,

Su ke wa maza azaba,

Gashin masara su ke wa,

Mazan aure na sunna,

Ko na gurguru don su burge,

Maƙota dangi ƙawaye.


Wasu ko liƙin gurasa,

A tanderu su ke wa,

Mazansu a kodayaushe,

Wai kar su sake su miƙe,

Ƙafa balle su sami,

'Yar damar ƙara aure.


Wasu ko matan na kirki,

Salihan bayi na Allah,

Mijinsu a kulliyaumin,

Sarki ne shi gidansa,

Sai yadda ya so su ke yi,

In ya ce zauna su zauna.


Baya magana su sauya,

Baya tari su tanka,

Ko ya ajje kara su taka,

Zuga gorin ƙawaye,

Bai sa su su sauya hali,

Sun fi gane su raya sunna.

Malam Khalid Imam
08027796140
khalidimam2002@gmail.com

Post a Comment

0 Comments