Ticker

6/recent/ticker-posts

2023 Ranar Waƙa

Wannan na ɗaya daga cikin jerin waƙoƙin Malam Khalid Imam da a kullum suke faɗakarwa da ilimantarwa da nishaɗantarwa. Yana taɓo fannoni daban-daban a cikin waƙoƙinsa, ciki har da abubuwan da suka shafi lamuran yau da kullum.

Rana ce yau ta waƙa,

Su azanci ne da kansu,

Ke taka rawa da baiti,

Awo jigo ma'auni,

Su amsa - amo da ɗango,

Yau su ne masu liƙi,

Bikin rana ta waƙa,

Su ne ƙirjin biki yau,

Ta ya wasu za su taka,

Suna gefe a raɓe?


Yau rana ce ta waƙa,

Jinjina yau nai wa waƙa,

Ina godiya Allah,

Cikin baiti a waƙa,

Nakan yabi Ɗan Amina,

Cikin harshe na waƙa,

Iyayena dukkansu,

Matayena da 'ya'ya,

Abokai malamaina,

Nakan waƙe a waƙa.


Ba shakka zamanin da,

Mutanen da da gaske

Basa sakaci da waƙa,

Ko da an shata daga,

Sarakai jaruman da,

Waƙa ke kamba ma su,

Su yi jarunta a yaƙi,

Su sai wa ƙasa mutunci,

'Yanci daraja ga kansu,

Su da mataye da 'ya'ya.


Malamai da yawa sukan yi,

Wa'azi nuni da hujja,

Da baitoci na waƙa,

'Yan siyasa masu mulki,

Ba sa sakaci da waƙa,

Akwai ilimi a waƙa,

Madubi ce ta duba,

Akan faɗakar da waƙa,

A nishaɗantar da waƙa,

Waƙa ta zarce raini.


Illar cuta da ciwo,

Ta jahici da kazanta,

Amfanin ai ta tsafta,

Ta jiki da gida muhalli,

Waƙa na fayyace su,

Domin jama'a su waye,

Su taimaki kawunansu,

Noma kiwo sana'a,

Su bar bacci da yin su,

Su amfanar da kansu.


Mace kyakkyawa da waƙa,

Akan yabi kyanta sosai,

Darajarta a kambamata,

Ta kere sa'a a tsara,

Saurayin da ya ke da himma,

Ko mai farce na susa,

Waƙa na sa shi kyauta,

Himma ƙwazo ya ƙara,

Waƙa dokin kilisa,

Rigar sawa ta ƙaye.


Haka masu kuɗi da mulki,

Sakiri a da da yanzu,

Waƙa ke ba su ƙima,

Jama'arsu su so su sosai,

Masu ƙinsu su daina ƙin su,

Waƙa na sanya sulhu,

Maƙiyan juna su shirya

Su bar rigima da juna,

Waƙa dai rayuwa ce,

Don hoton rayuwa ce.

Malam Khalid Imam
08027796140
khalidimam2002@gmail.com

Post a Comment

0 Comments