Kar ku ce ba na posting ɗin da za ku ƙaru...
Yau zan kawo muku yadda ake shara😊
Abubuwan buƙata:-
1-Tsintsiyar laushi ko ta kwakwa
2-Abin kwashe sharar
3-Sai ke kan ki mai sharar.
Da farko za ki kimtsa kanki da bujen wando saboda kifi sakewa, sannan ki dauko tsintsiyarki ki riƙe ta a hannunki na dama, in Kuma ke bahaguwa ce, sai ki riƙe ta da haƙu, sai ki ajiyeta kidan huta, ki kalla girman gurin da za ki share😞😒.
Sannan ki miƙe tsaye, sai ki durƙusa ki riƙe gwuiwarki da hannu daya, hannu daya Kuma tsintsiyarki. Sai ki yi Bismillah ki fara😊.
Kina cikin yi in kika gaji sai ki ɗan zauna ki ci gaba da yin sharar a haka, kina yi kina matsowa har Allah ya kawo ki inda zaki tattara shararki, note that a gurin tattara sharar akwai buƙatar zama saboda iska kar ta wargatsa miki aikin alkairinki yake Yar uwa😁😍.
Bayan kin kwashe sharar tsaf sai ki je ki zuba ta a ma'adanar zuba shara, sannan ki mayar da tsintsiyarki ma'adanarta, sai ki gangara bakin fanfo ki wanke hannu ki dawo ki kalla abinda kika yi ki yi murmushi 😌😊.
Sannan ki zauna duk yaron daya fara batawa ki jibgeshi tunda bashi da tausayi🏃😂
Tammat bi hamdillah an kammala wannan sharar.🚶🏾
0 Comments
Post your comment or ask a question.