Ticker

6/recent/ticker-posts

Wacce Addu'a Zan Yi Na Kare Kaina Daga Mummunan Sha'awa?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Malan ina son a koyamin addu'ar dazan kare kaina daga mumuna Sha'awa wallahi ina cikin tashin hankali nagode atemakamin.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam: Ni Ban San Wani Addu'a da yakamata ka kama ka ringa Yi Domin Sha'awar ka ya dena ba. Domin shi Sha'awa wani abu ne wanda Allah ya Halitta shi dole idan kakai Wannan Lokacin kake jin shi. Maganin abin shi ne ka bi Umurnin Manzon Allah da yake Cewa Yaku Taron Matasa idan Ɗayan yana da lafiya sannan yana da Wadata to ya yi Aure.

Lafiyar Shi ne Sha'awar da ke Damin mutum idan mutum yana jin zai iya yin Aure sannan zai iya biyawa Matar buƙatan ta na Jima'i, Annabi ya ce Kayi Aure, yin Hakan shi ne zai cire ma duk wani Sha'awar da ke Damin ka, sannan zai tsare ka da fadawa halaka na Zina,

Wadata Shi ne idan Allah ya hore ma Kuɗin da zakayi Hidima kama daga bayar da Sadaki kayan Aure da sauran su daidai Gorgodon Yadda za ka iya. Annabi ya ce Kayi Aure, hakan shi ne zai kare ka daga Dukkan komai na Sha'awar ka. Annabi Muhammad Mai Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata Agare Shi, ya ce idan kuma duk hakan bai Samu ba, to Sai mutum ya kama yin Azumi domin shi Azumi shima yana cire Sha'awa, idan Mutum Ya Koshi Ne Zai ke Jin Sha'awa na Damin Shi. Da yawan cin Abinci Kala Daban-daban. amma idan mutum na Famada Yinwa ta yaya Zai Ringa Jin Sha'awa? Shi ya sa Annabi ya ce a yi Azumi, Domin Shima yana Cire Sha'awa. Ka Kama Yin Azumin Litinin Da Alhamis, Ko Kuma Azumin Annabi Dawud A.S Yau Kayi Gobe Ko Huta, Jibi Kayi Gata Ka Huta.

Sannan Ka Dena ko Ka Rage Kallon Hotunan Batsa, ko Videos Na Batsa, ko Films da Ana Yawan Rumgume Mace ana Kiss da ita, ko ana Shiga Daki da Sunan anyi Aure Da Mace Duk a Films, ko Hira na Motsa Sha'awa, ko Zama da Mace a Waje Guda, da rage yawan cin Abinci Kala Daban-daban, kake Cin Kala ɗaya Kawai, Duk Waɗannan Abubuwan ka Kaura Ce Musu ka Dena su idan daman Kana Yin su, in ko bakayi Shikenan, karfin Sha'awar ka ne yakai Haka. Ka Dena zubawa mace Ido Kallo ɗaya Manzon Allah ya ce ayi, amma sai a yi ta Zura ido a jikin Mace daga Sama Har Kasa, yaya Sha'awar ka bai tashi ba sai kace kai Mala'ika ne. idan Mutum ya ce ɗaya Manzon Allah ya ce a yi Saurayi sai ya ce to ai Har Yanzu bai Ketta idon shi ba. Abin ya dawo kamar me. To duk Wannan ka kiyaye Su.

Sannan ka Tsai da Ibada Sallolin Farillah a kan Lokutan Su, kana Yin Su da ikkilasi kana mai yin Tawassuli dasu, da Yawaita Yin Nafilan Dare ko Na Rana da Yawaita Yin Karatun Al Ƙur'ani Mai Girma, da Yawaita Yin ISTIGIFARI. Insha Allahu idan ka Dage da Wannan Sai Allah ya Taimake ka komai naka ya zo Normal.

Shawaran da Zan Baka Shi ne idan Kanada Lafiya da Wadatar Kuɗi Kayi Aure, idan Kanada Kuɗin da zai kai ka Auri Budurwa to Kayi Gaggawan Yin Aure shi ne ya fi Dacewa, idan Baka da Kuɗin Da za ka Auri Budurwa, akwai Bazaura Sai ka Aure ta. Shi ya sa abin akayi shi Hawa biyu idan baka da Halin Wannan ga Wannan, Allahu Swt ya gama mana komai Sai dai idan bakayi Niyya ba kawai. Kace sai Wacce kake so idan ba ita ba kai babu aure, kuma kullum kana cikin Sha'awar ta idan Kayi wasa za ka fada Zina, Kayi aiki da abin da karfin ka ya baka bawai abin da karfin ka bai baka ba. Idan duk Wannan bai samu Sai ka bi Abin da na fada a Sama kama Yin Azumi da Sauran ibada sai Allah ya kawo ma Mafita. Amma yin Aure shi ne the Best Solution da zai cire mai komai ka dawo Normal. Dafatan Ka Gane?

WALLAHU A'ALAM.

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/L8l4xHCd7wUG5xZEmvBbzB

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments