Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Azumin Me Kallon Hotunan Batsa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Mallam mutum ne yana kallon hotunan mata a waya (hanset) kuma yana azumi, bayan yaje ya yi fitsari sai ya ga maziyyi ya fito masa, to ya matsayin azuminsa yake?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Mutum yana azumi kuma ya tsaya yana kallon tsaraici ai baka kyauta ba, kuma dama shi ya sa malamai suka kasa azumi mataki-mataki akwai azumi na gama gari akwai azumi na ke6antattu, akwai azumi na ke6antattun-ke6antattu.

1- Azumin gama gari shi ne idan anayi ba za a ci ba ba za a sha ba baza a yi jima'i ba amma kuma sauran shiririta ba za a kauracemishi ba, kamar kallon hotana na batsa, ko kallan mata a kan hanya suna hucewa, dai-dai sauran abubawa da suke haramun.

2- Azumin ke6antattu kuwa su ne wadanda suna azumin bakinsu yana azumi, farjinsu yana azumi, idon su yana azumi, kunnansu yana azumi, baza su saurari zance na batsa ba ko munmunan zance ba, haka nan hannunsu ba zai ta6a haramun ba, haka nan kafar su bazata taka zuwa gurin da yake haramun ba, wannan dai shi ne azumi na ke6antattu.

3- Shi kuma azumin ke6antattun-ke6antattu shi ne yanda bakinsu yake azumi haka nan ga6o6insu suke azumi, tunaninsu ma azumi yake zuciyar su azumi take, kai duk wani ga66ai nasu azumi yake.

Dan haka wai a ce mutum yana azumi, har yakai ga kallon hotunan batsa a waya har takai ya zubar da maziyyi, a gaskiya hakan da aka yi an yi ɓarna, saboda haka a hukuncin malikiyya dai idan har haka takasance da mutum to zai rama wannan azumin, kuma bawai zai cigaba da cin wani abu ba a'a zai cigaba da kamun bakinsa har a sha ruwa, sai kuma bayan sallah ya rama.

Idan kuma kullum haka yake yi to duk zai ramasu bayan an gama azumin, kuma idan har ya zo da tsautsayi aka zubar da maniyyi to wannan sai ramuwa da kaffara, ma'ana za a rama wannan kuma a yi na kaffara guda 60 ba hutuwa.

WALLAHU A'ALAM

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/L8l4xHCd7wUG5xZEmvBbzB

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments