Ticker

6/recent/ticker-posts

Allah Idan Na Kara Saba Maka, Kar Kakara Yafe Min Kuma Ka Sa Ni A Wuta

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahamatullahi. Ina wuni malam ya aiki? Tambayata a nan ita ce malam mutum ne yana aikata saɓon ALLAH kullum idan ya aikata yana tuba kuma ba da san ranshi ba harya ce ya ALLAH idan na ƙara saɓa maka kar ka kara yafe min kuma ka sa ni a wuta sabida bayaso ya saɓawa ALLAH yafadi hakan, kuma yazo yakara saɓawa ALLAH zai yafe masa idan ya tuba kuma ba zai sa shi a wuta ba.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Waalaikumussalamu. To Bayin Allah Hakika Allah maɗaukakin sarki yana yafe kowane irin laifi Amma baya yafe laifin shirka dukkan wanda ya mutu yana shirka da Allah to Allah ba zai yafe masa ba, kuma zai dawwama a cikin wutar jahannama kamar yadda Allah ya faɗa a cikin Al'kurni mai tsarki. Allah ta'ala ya tsare mu.

Sabida haka In sha Allahu, Allah zai yafe masa kuma ba zai sa shi a wuta ba matukar ba shirka ya mutu yana aikatawa ba ya wajaba ya tubarwa Allah a bisa wancan bala'in da yake nema ya jajubowa kansa, Sannan kuma ya kamata ya sani dukkan Ýan adam Allah ya kaddara mana zamu dinga saɓa masa, Matukar mutum ba Annabi bane kuma ba mala'aka bane, to dole ne sai ya aikata saɓon Allah, Annabawa da mala'ikune kaďai basa aikata Saɓon Allah domin su tsarkakakkune Allah ne ya zaɓe su ya fifita su kuma ya tsarkakesu a cikin bayinsa, Sabida haka ya kamata yasan cewa shi be isa ya ce ba zai kara saɓawa Allah ba tunda shi ba Annabi bane kuma ba mala'ika bane, kunga kuwa bai dace ya fadi waccan mummunar kalmar daya fada a baya ba, Amma kuma ya kwantar da hankalinsa in Sha Allahu, Allah ba zai kama shi da waccan maganar da ya yi ba.

Hadisi ya inganta daga Manzon Allah cewa: YA CE: IBLIS YA RANTSE WA ALLAH AKAN SAI YA HALLAKAR DA BIL ADAMA MUDDIN SUNA RAYE, SAI ALLAH YA RANTSE MASA AKAN BA ZAI GUSHE YANA GAFARTA MUSU BA MUDDIN SUNA ISTIGFARI.

{Musnad Ahmad}

A wani hadisin kuma manzon Allah ya ce: DUKKAN ÝAN ADAM MASU AIKATA ZUNUBI NE MAFI ALKHAIRIN CIKINSU su ne MASU TUBA.

{Sunan Ibn Majah}

A wani hadisin kuma manzon Allah ya ce: TUBA DAGA ZUNUBI ITA CE YIN NADAMA AKAN ZUNUBIN, TARE DA NEMAN GAFARAR ALLAH.

{As-saheeha 1208}

A wani hadisin kuma manzon Allah ya ce: YIN NADAMA AKAN ZUNUBI TUBANE KUMA WANDA YA TUBA DAGA ZUNUBI KAMAR WANDA BAI AIKATA ZUNUBIN BA NE.

{sahihul Jami'i 6803}

Sabida ďan'uwa yanzu ya isa ka fahimci cewa baka isa kace ba za ka yi saɓon Allah ba saidai abinda ake so kakai makura wajen nisantar saɓon Allah duk wata hanya da kasan tana kai ka zuwa ga aikata saɓon Allah, sannan kuma ina maka bushara da cewa ita kanta shiga damuwar da kake yi a duk lokacin da ka tsinci kanka cikin aikata wani zunubi, Alamune da suke nuna cewa akwai imani a tare dakai kuma ina fatan sai an wayi gari wataran ka dena aikata laifin, Amma kar yadda ka dinga yiwa Allah al'kawarin cewa idan ka sake saɓa masa ya saka ka a wuta Yin hakan akwai hatsari kuma munana zato ga Allah ne, Sabida haka lallai ka kiyaye wannan kaidai ka dage wajen neman shiriyarsa tunda shiriyar taka ba a hannunka take ba, Amma kar ka yadda kuma ka dinga raya cewa laifin da kake aikatawa ba a bakin komai yake ba, domin daga lokacin da ka ɗauki zunubi ba a bakin komai ba to babu shakka imaninka ya yi rauni kuma duk mai daukan zunubi ba a bakin komai ba tsatsa ta riga ta cika zuciyarsa, Allah ya tsaremu.

 

Yakai ďan uwa ka sani cewa shi Allah maɗaukakin sarki me gafara ne kuma me rahama ne Sannan kuma yana farin ciki kuma yana maraba da bawansa yayin da bawan ya tuba daga aikata zunubin da yake aikatawa, Sabida haka Shi Allah yana yafe ko wane irin laifi kai koda mutum shirka yake aikatawa to idan ya tuba ya nisanci zunubin Allah zai karbi tubansa matukar bai zo gargara ba Ma'ana matukar lokacin tuban be 'kure masa ba.

 

Sannan kuma Kaga hadisan da suke sama sun nuna mana cewa idan mutum ya yi nadamar aikata wani zunubi to ita kanta nadamar da ya yi na aikata zunubin alamar tuba ce idan kuma ya tuba ya yi istigfari to Allah zai shafe zunubansa zai dawo kamar be taɓa aikata zunubin daya aikata a baya ba, Ammafa wannann iya zunubin dake tsakanin bawa da mahaliccinsa ne Allah yake yafewa banda laifin wani akan wani. Da wannan nake maka albishir indai ka nisanci laifin to Allah zai yafe maka abinda ka aikata a baya musamman idan ka lazimci istigfari, karatun al'kur'ani salatin annabi dasauran ayyukan alkhairi kuma ka lazimci yin addu'o'in shiriya kamar faďin

 

« ﺍﻟﻠﻬُﻢَّ ﺇِﻧِّﻲ ﺃَﺳْﺄَﻟُﻚَ ﺍﻟْﻬُﺪَﻯ ﻭَﺍﻟﺘُّﻘَﻰ ﻭَﺍﻟْﻌَﻔَﺎﻑَ ﻭَﺍﻟْﻐِﻨَﻰ »

ALLAHUMMA INNIY AS'ALUKAL HUDAH, WAT TUKAH, WAL AFAFA, WAL GINAH.

Ma'ana: "Ya Allah ina rokonka shiriya da takawa da kamewa da wadata".

« ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺇِﻧِّﻲ ﺃَﺳْﺄَﻟُﻚَ ﺍﻟْﻬُﺪَﻯ ﻭَﺍﻟﺴَّﺪَﺍﺩ ».

ALLAHUMMA INNIY AS'ALUKAL HUDAH WAS SADAD.

Ma'ana: "Ya Allah ina rokonka shiriya da dacewa".

Hakanan ka dinga karanta wannan addu'ar yayin da kake sallah bayan kan ďago daga sujjadar farko kafin ka koma sujjada ta biyun:

اللّهُـمَّ اغْفِـرْ لِي، وَارْحَمْنِي، وَاهْدِنِي، وَاجْبُرْنِي، وَعَافِنِي وَارْزُقْنِي وَارْفَعْنِي

 

ALLAHUMMAGH-FIR LEE, WARHAMNIY, WAHDINIY, WAJBURNIY, WA'AFINIY, WARZUKNIY WARFA'NIY.

Ma'ana: Ya Allah! Ka gafarta mini, ka ji kai na, ka shirye ni, ka wadata ni, ka ba ni lafiya da tsira daga musifu, ka azurta ni, ka ɗaukaka ni.

WALLAHU A'ALAM

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments