Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarihin Maitatsine

Wannan na ɗaya daga cikin jerin waƙoƙin Malam Khalid Imam da a kullum suke faɗakarwa da ilimantarwa da nishaɗantarwa. Yana taɓo fannoni daban-daban a cikin waƙoƙinsa, ciki har da abubuwan da suka shafi lamuran yau da kullum.

Muna yara ƙanana,

A kai Yaƙin Tatsine.


An ce shi Maitatsine,

Ƙofar Wanbai ya zauna.


Sansani ya yi kan a farga,

Yara da yawa ya tara.


Shahuchi ya ke fito wa,

Yana wa'azi da Yamma.


Kafin a Kano a farka,

Ya yi ƙarfi Maitatsine.


Maganarsa fa ɗalibansa,

Kaɗai su ka ji su ɗauka.


Don a gun yaran Tatsine,

Ba mai ilimi irinsa.


Malami a Kano kamarsa

Wai babu irin ya Malam.


In ya ce gwamna da sarki,

Su ɗauko, sai su danna.


In ya ce musu ga wuta can,

Ku faɗa, sai su faɗa.


Lokacin a Kano iyaye,

Suna lura da 'ya'ya


Ban mantawa da Yamma,

Muna wasa da yara.


Aka tattara kawunanmu,

Sai gida baki ɗayanmu.


Ba wanda ya sake leƙo,

Ko soro lokacin nan.


Addu'a da kular iyaye,

Ta kassara Maitatsine.


Saɓanin yau iyaye 

Su ne 'ya'yan da gaske.


Ba ruwansu da sa idanu,

Kan yara me suke yi.


Kun ji labarin Tatsine,

Na Marwa Kano ta karshi.


Domin a Kano ya sheƙa,

Lahira don da da manya.


Tabbas a Kano da manya,

A da can masu kishi.


Masu kishi masu lura,

Masu tarbiyya ga yara.


Malam Khalid Imam
08027796140
khalidimam2002@gmail.com

14/03/2023

Post a Comment

0 Comments