Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Ƙi Yarda A Yi Zina Da Ita Har Aka Kashe Ta

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Mace ce aka tilastawa za'ayi zina da ita taki yarda har aka kashe ta a kan hakan, ta yi abun da ya dace ke nan?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Toh a nan dama tana da za6i dayan guda biyune walau dai ta yi riko da Sauki ko kuma ta yi riko da tsanani domin asadda taga abun ya ta'azzara toh idan ba za ta iya yarda ta rasa rantaba tana ganin cewa gara tabari a yi abun da ake so ayidin da ita toh a nan seta bari a yi ɗin. amma ta kyamaci abun a zuciyarta insha Allahu Allah baze kamata da wannan lefinba. In kuma tana ganin cewa a kan ta tsaya hakan tafaru da ita gara har a ce ta rasa ranta toh a nan kuma idan ta rasa ran nata akwai yiwuwar Allah ze iya ba ta darajar masu mutuwar shahada domin Annabi (s.a.w) ya ce: Wanda aka kashe shi a wajan ƙoƙarin kare mutuncinsa toh shahidi ne shi, ka ga lura da wannan hadisin se mu ce ita ma wannan matar muna kyautata mata zaton cewa insha Allahu ta yi shahada.

Allah ya sa mu dace

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments