Ticker

6/recent/ticker-posts

Addu'ar Bayan Kiran Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahamatullah taallah wabarakatuh, malam Allah ya saka muku da Alheri, bayan haka malam ina da tambaya tambayata ita ce: Don Allah malam wacce irin addu'a ingantacciya mutum zai iya yi bayan kiran sallah?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Waalaikumussalam, Wannan Tambaya Tana da Matukar Muhimmaci Ga Duk Wani Musulmi, Kasancewar Faɗin Annabi Cewa Duk Wanda ya yi Addu'a Wannan Lokacin ba a Mayarda Ita, Haka Daga Cikin Falalolin Kiran Sallah Idan Mutum Ya Kasance Yanabin Dokokin yayin da Ake Kiran Sallah shi ne, Ze Samu Ceto Daga Annabi Da Samun Yima Sheda Ta Alkairi Daga Abubuwanda Baka Zataba A Ranar Alkiyama. Abubuwanda Ake so Mutum ya yi Lokacin da Ake Kiran Sallah Domin Samun Wadannan Falaloli shi ne:

1. Tsayawa Da Duk Wani Abu Da Mutum Yake yi Da Kashe Duk Wani Sauti Dayake Kusa da shi (Koda Karatun Ƙur'ani Ne) Domin Sauraron Kiran Sallah Har A Gama.

2. Maimaita Duk Abin da Me Kiran Sallah Ya Fadi, Sai dai Wajen Faɗin ''Hayya alal Salah, Hayya alal Falah'' Sai Shikuma Me Bi Zaice, ''La Haula wala Ƙuwwata Illa Billah''

 

3. Faɗin Wannan Addu'ar Bayan Kiran Sallah “Ashhadu An La’ilaha Wahdahu, La Sharika lahu, Wa Anna Muhammadan Abduhu Wa Rasuluhu, Raditu Billahi Rabban, Wabi Muhammadin Rasulullah, Wabil Islami Dinan”

 

4. Yin Salati Ga Annabi Bayan Kammala Wannan Addu'a Data Gaba ta Da Fadin ''Allahumma Rabba Hazihid Da'awatit Tammati, Wassalatil Ƙa'imati, Ati Muhammadanil Wasilata wal Fadilah, Wab'ashu maƙaman mahmudanil lazi wa'addahu”

5. A Ƙarshe Sai yi wa Kai Addu'a Kowace Iri, Faɗin Annabi Cewa, Haƙiƙa Addu’a Tsakanin Kiran Sallah Da Iƙama ba a Mayar Da Ita”

WALLAHU A'ALAM.

🏼 Abu_Zhahrah.

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ 

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments