Ticker

6/recent/ticker-posts

Matata Ta Rasa Ni'imarta Bayan Ta Haihu

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, malam barka da ƙoƙari, Allah ya saka da mafificin sakamako. Iyalina ce ta rasa ni'imar ta, da kuma sha'awarta tin bayan haihuwar ta da ta yi sati 4 da suka wuce. Amma haihuwar ta biyu ce kuma a ta farko ba ta fuskanci irin hakan ba. Malam mene ne shawara?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikumussalam. Yawanci 70% na mata rashin samun natsuwa azuciyoyinsu ko kuma rashin kyautatawa daga mazajensu da yawan damuwa agidan aure da rashin cin abubuwa masu gina jiki da ayyukan wahala dakuma infection su ne sanadiyyan da suke dauke musu ni'ima sai kuma rashin iya sarrafa macen daga wurin mijinta wannan yanasawa mace tacire abin aranta har yakaiga tana bushewa. to inhar akwai ɗaya daga cikin abin da na lissafa dole sai an yi maganinsa kafin ni'ima tadawo, Amma idan harka tabbatar da babu ɗaya daga cikin abubuwan dana lissafa to asami sassaken ɓaure sai asami citta, kanumfari, masoro dakuma mazarkwaila, sai ahaɗasu atafasashi sosai Inya huce sai tana yawansha in tasaka a fridge zai kwana biyu tana sha kafin tasake tafasa wani.

Ta samo, kwakwa, da kankana da dabino ta yi blending nasu sai tasaka madara tana sha Amma Dan ALLAH kar tana amfani da magunan mata barkatai babu abin da suke haifarwa daga ƙarshe sai nadama.

WALLAHU A'ALAMlam

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments