Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Zan Iya Aje Azumi Idan Mijina Yana Buƙatata?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum ina da tambaya Mace ce tadau Azumi sai mijin ta ya kira ta ya ce mata yana zuwa kuma in ya zo ba kwana zai yi ba sai ya ce ta Aje Azumin shin za ta bishi ne ta Aje ko kawai takai Azumin ta?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikumussalam warahmatullah wabarakatuhu

To hadisi ya tabbata daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallam cewa "kada mace ta yi azumi alhalin mijinta yana nan, awasu ranaku inba na ramadan ba, saida izininsa" Bukhari yarawaito ahadisi mai lamba 5195, Muslim kuma 1026.

Amma idan miji bayanan mace tana iya daukar azumin nafila, idan kuma tana tsoron zai iya dawowa kowane lokaci a irin wannan zamanin da akwai wayar salula, za ta iya kiranshi domin kawarda kokwanto, amma ko da ba ta kiraba za ta iya yin azuminta, amma idan yadawo ya buƙace ta to kawai ta karya azumin, domin amsa kiransa wajibi ne indai ba tare da wata lalura ba, shikuma azumin ba wajibi ba ne

Allah ya sa mu dace

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments