Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Raba Kwana Tsakanin Miji Da Matansa, Idan Ɗayan Matar Ta Yi Tafiya Ta Dawo

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Allah yakarawa Malam lafiya, dan Allah tambaya nake. Idan namiji yana da mata biyu sai ɗaya ta yi tafiya tayo kwanaki ta dawo, tambayata a nan ita ce ranar da ta dawo wane daki ya kamata mijin ya kwana?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa'alaykumussalam. Mu'amala ta aure da zamantakewa abin da shari'a ke buƙata a cikin su shi ne yin adalci, aduk yadda mai gida da iyalansa suka tsara yadda za su zauna matuka an kiyaye ka'idar (Kada a yi cuta kuma kada a cutar) toh babu laifi, don haka ba laifi don ya shiga dakin wadda ta yi tafiya duba ga an dade ba a haduba.

Wallahu A'alam

Amsawa🏻

Malam Nuruddeen Muhammad Mujaheed

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments