Abin da ya wajaba ga mace musulma shi ne, ta sanya tufafin da zai suturce jikinta, in ban da fuska da tafin hannu a wajan wasu malaman suna ganin fuska al'aura ce.
Don haka ita ma ya wajaba a rufe ta, tun da a nan kyawun mace yake, sannan kayan da zatasa su zama masu kauri, baya halatta ta yi ado inba a cikin gidan mijinta ba, ko tare da muharramanta.
Suturar mace
musulma ba a so ta yi kama da kayan maza, kamar yadda ba a so su zama kayan da
za su ja hankali, ko waɗanda aka fesa musu turare
mai ƙarfi.
Sannan mutuƙar Abaya ko jallabiyya ta suturce jiki yadda ya kamata, ba ta matse jikin mace ba, to za ta ɗauki matsayin hijabin da ALLAH daManzonsa {s.a.w} suka yi umarni.
Don neman ƙarin bayani duba:
Majmu'ul-fataawa 22/110 da Hijabul- Mar'atulmuslima
shafi na: 54 zuwa 67.
ALLAH shi ne mafi sani.
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
Post your comment or ask a question.