Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Halatta Na Yi Wa Mijina Ƙarya Dan Na Samu Saukin Saduwa Da Shi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalama alaikum Shin Ina da laifi dan na yi karya wa miji na ba ni da Lfy dan kada ya kusance ni? Kullum yana zuwa da buƙatarsa ba ya tausaya min.

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa,alaikumussalam ALLAH sarki wasu matan sunata kawo Ƙara a kan mijinsu, seya yi wata huɗu wasuma shekara 5 wasun ma kam har sun manta lokacin.. Ga wata ta samu kuma tana ƙi 😂

Yana daga cikin riƙe alƙawarin aure, shi ne biyawa miji buƙatansa, a duk lokacin da ya nemeki, ko da kina al-ada, za ki biyamar buƙata amma ban da saduwa ta farji dubura kam dama haramun ne!!!

 Sedai kinemi shawaran shi, idan yana da hali ya ƙara aure! Idan kuma baida hali, kekuma ba za ki iya juran yadda yake miki ba, za ki iya neman ya sauƙaƙe miki. Seki biyashi sadaki ya yi wani Auran.

 

Amma idan kikayi Ƙarya tofa mala'iku za su hau aikin su na tsinuwa. Ina dai baki shawara ki jure kiyi haƙuri da yanayin sa, kiriƙa mar fatan samun kuɗin Ƙara aure, idan kika ƙuntata har zina ze fara idan ba ALLAH ne ya shirye shi ba, daganan seya ebo muku cuta.

Sannan karki biye Shaiɗan, soyake ya rabaki da mijin ki. Sannan alheri ne dan ya nemeki alamar kinsamu karbuwa a wajen sa, kuma muna miki tsammanin samun yardan ALLAH. Sedai hakan baze hana ki dan shawarceshi daya riƙa dan sassautamiki, amma kinema a ya yin yadda ya dace, kada kiyi yadda ze fusata, har ya Ƙaurace miki sama da yadda ba za ki iya jura ba!!!

Sannan mazaje yana da kyau ku gane cewa, yawaita jima'i batare da sauran bautan ubangiji ba, hakan yana nuna alamace irin ta rayuwan dabbobi, dan suma aikin su ke nan, suci su yi jima,'i su kwanta..... Yawaita Jima'a yakan iya Rage ƙarfin ma'aurata, idan ka kasance muzakkari to kadage ka Ƙara Aure matuƙar kanada hali!! ida bakadashi kuma ka riƙa hikima, wajen saduwan kar-ka yawaita saduwa da ita ta farji, ka riƙa biya buƙatu ka ta sauran Sassan jikinta ban da Dubura dan haramun ne!

Allah ta'ala ya sa mu dace.

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments