𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam nice ina da miji a duk lokacin da zan zo kusa da shi sai ya ce min barci yake ji, ai shari'a ta hana na dameshi, a haka za mu yi kusan wata ba abin da ya shiga tsakanina da shi, Allah taimaki malam mene ne mafita?
𝐀𝐌𝐒𝐀👇
Wa'alaikumussalam, Ki tambaye shi dalılin da ya sa yake
yin hakan, zai iya yiwuwa kin ba ta masa rai ko kuma akwai Wata matsalar, amma
ta hanyar tambaya ko shigar magaba ta lamura za su iya fitowa fili.
Sharia ba ta halattawa namiji ya ki saduwa da matarsa
ba da gangan, saboda nau'i ne na cutarwa, yana dağa cikin manufofin aure
katange ma'aurata daga kallon haram.
Allah ta'ala ya sa mu dace
Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa
Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
Post your comment or ask a question.