Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Halatta A Ɗaura Aure A Watan Ramadan?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamun alaikum, gafarta malam ina da tambaya, shin wai akwai wani nassi da ya ce babu kyau a yi aure a watan ramadan, kuma shin ya halatta mutum ya yi zance da wacce yake fatan aura?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus salam Warahmatulah wabarkatuh.

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah.

 To babu wani abu a Musulunci da ke nuni da cewa haramun ne a yi aure a watan Ramadan, ko saboda wai watan Ramadan ne, ko kuma a wani wata. Don haka, musulunci ya halatta yin aure a kowace rana ta shekara.

Amma mai azumin ramadana dole ne ya nisanci ci da sha da saduwa tun daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana. Don haka idan har zai iya kame kansa kuma ba a tsoron ya aikata abin da zai karya azuminsa, to babu laifi ya yi aure a Ramadan.

Da alama kamar yadda muka sani masu sababbin aure a watan ramadan yawancin su ba za su iya yin hakuri da nisantar matansu ba a tsawon yini, kuma akwai tsoron kada su aikata wani abu da aka haramta kuma su fada cikin zunubi mai girma, wanda a kan hakan. wajibi ne a rama azumin ranar tare da kaffara mai tsanani, wanda yake ko dai a ‘yanta bawa; idan ba za a iya hakan ba to sai su yi azumin wata biyu a jere; idan kuma hakan shi ma ba zai yiwu ba to sai su ciyar da miskinai sittin (kamar yadda shari'a ta yi bayani). Idan kuma suka sake yin wani jima'i a cikin kwanaki ramadan ɗin, to dole ne su sake maimaita wannan kaffarar. Ma'ana, idan suka yi jima'i sau 2 ko 3 to za su yi kaffarar 'yanta bawa 2 ko 3, ko azumin wata 4 ko 6 a jere, ko su ciyar da miskinai 120 ko 240 da sharadin idan ba za su iya na farko da na biyu ba.

Fatawa a kan azumin kaffara mun jima da amsawa za a iya duba site din mu don bincikawa.

Shawararmu ga wannan mai tambaya ita ce, idan akwai tsoron ba zai iya kame kansa ba, to ya jinkirta aurensa har sai bayan Ramadan, ya shagaltar da kansa a cikin Ramadan, da ibada, karatun Alkur’ani, addu’a. ƙiyamul layl, da sauran ibadu.

Dangane da hukuncin yin zance/hira a watan Ramadan ga wacce yake son ya aura, mun riga mun amsa wannan tambayar ita ma. Da fatan za a duba a shafukan mu.

Kuma Allah ne Mafi sani.

📚Shashen Fatawa bisa Ƙur'ani, Sunna da Maganganun Magaba ta na ƙwarai.

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Eub2uLrV18T4vHJcƙRDkPZ

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments