Ticker

6/recent/ticker-posts

Ciyarwa

Wannan na ɗaya daga cikin jerin waƙoƙin Malam Khalid Imam da a kullum suke faɗakarwa da ilimantarwa da nishaɗantarwa. Yana taɓo fannoni daban-daban a cikin waƙoƙinsa, ciki har da abubuwan da suka shafi lamuran yau da kullum.

Ya al'ummar Ma'aiki,

Kar mui sakacin ciyarwa.


Bana ga Ramadana ya zo,

Mu dage yin ciyarwa.


Loma ta abinci bayar,

Rabbana na son ciyarwa.


Falala buɗi ka ke so,

Sirrinsu yana ciyarwa.


Mai son koyi da Manzo,

Ya daina gudun ciyarwa.


Lahirarka idan kana so,

Ka gyara kai ciyarwa.


In ba ka son abota,

Da talauci kai ciyarwa.


In ba ka son ƙiyayyar, 

Mutane kai ciyarwa.


Igiyar ƙullin zumunta,

A dangi ce ciyarwa.


Ruwan wanke ƙiyayya,

Da gaba yin ciyarwa.


Dausayin wanzar da ƙauna,

Ta juna na ciyarwa 


Ƙima daraja da mutunci,

Neme su cikin ciyarwa.


Ladan azumi da bonas,

Ana ba mai ciyarwa.


Ruɓi ninki na khairan,

Nace dage ciyarwa.


Zuciyarka ka so ka 'yanta,

'Yanta ta da yin ciyarwa.


Huɗubar rowa ka ke ƙi,

Guje ta da yin ciyarwa.


Buƙatu ne da kai him,

Neme su da yin ciyarwa.


Ko da matsala ka faɗa,

Nemi sauƙi kai ciyarwa.


Shaiɗan ne zaka kora,

Kore shi da yin ciyarwa.


Walwala nutsuwa ta zuci,

Ka ke so kai ciyarwa.


Soyayya ce ka ke so,

Kar ka manta kai ciyarwa.


Titin aljanna ɗoɗar,

Yana birnin ciyarwa.


Jahannama ce ka ke ƙi

Ka ƙi ta da yin ciyarwa.


Rayuwata Rabbu gyara,

Don albarka ciyarwa.


Arziki Allahu ba ni,

Domin falalar ciyarwa.


'Ya'yana Jalla shiryan,

Su ci albarka ciyarwa.


Zama gatana Ilahu,

A kullum don ciyarwa.


Tammat na sanya aya,

Ga nasiha kan ciyarwa.


Khalid Imamu ɗa ne

Na Maryam mai ciyarwa.


Mutan Makka na da himma,

Ba shakka gun ciyarwa.


Na shaida ni da kaina,

Babana yai ciyarwa.


Abbanina da ransa,

Bai fashin yin ciyarwa.


Juma'a kuwa har da kaji,

Ya ke sadaka ciyarwa.


A Kano aka haifi Khalid,

Garin da ake ciyarwa.


Loko lungu da saƙo,

A Kanonmu ana ciyarwa.


Azumin Ramadan ga shi,

Ya zo duka mui ciyarwa.


Malam Khalid Imam
08027796140
khalidimam2002@gmail.com

Post a Comment

0 Comments