Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mai Azumin Da Ya Ci Abinci Da Mantuwa

Idan mutum yana Azumi sai ya ci ko ya sha abin sha da mantuwa, azuminsa ingantacce ne, babu ramuwa a gareshi bare kaffara.

 Abu Huraira (R.A) ya ce:

 Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce:

Wanda ya manta ya ci ko ya sha lokacin da yake Azumi, to ya ci gaba da azuminsa, hakiƙa, ALLAH ne ya ci da shi ya shayar dashi.

[Bukhari ne ya rawaito].

Idan mutum yana Azumi sai amai ya zo masa ya amayar dashi, to babu komai a gareshi.

 Saboda faɗin Manzon ALLAH {s.a.w} da ya ce:

 Wanda amai ya zo masa lokacin yana Azumi ya amayar ba komai a gareshi, idan kuwa da gangan ya jawo aman to, ya rama Azumi.

[Tirmizi ne ya rawaito].

ALLAH shi ne mafi sani.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments