Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin mace za ta iya yin limanci?

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Amsa

Na'am ya halatta mace ta yi wa '‘yan uwanta mata limanci.

Nana A'isha da Ummu Salama (R.A) sun yiwa wasu mata limanci,

Nawawi ya ce Baihaki ya rawaito wannan hadisi a Sunan nasa, haka kuma Shafi'i a

Musnad ɗinsa da sanadi mai kyau, Almajmu'u (4/187).

 Haka kuma an rawaito cewa Annabi {s.a.w.} ya sanyawa Ummu-waraka (R.A) ladani, sannan ya umarceta da ta yiwa matan gidansu limanci, kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 491, kuma Albani ya kyautata shi.

Saboda haka dalilan da suka gabata sun isa hujja kan halaccin mace na iya yiwa matan unguwarsu limanci, idan dai ta zama tasan hukunce-hukuncen sallah.

Annabi {s.aw} yana cewa:

Wanda ya fi iya karatun Alƙur'ani shi ne zaiyi limanci.

[Muslim 1078].

Sannan idan mace zatayi limanci wa mata '‘yan uwanta za ta tsaya a

tsakiyarsu ne, bazata tafi gaba ta tsaya ba, kamar yadda liman namiji yake yiwa maza ba, in kuma su biyu ne, to sai ɗayar ta tsaya a damar wacce take limancin.

ALLAH shi ne mafi sani.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments