Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Mace Mai Jinin Istihala Za Ta Dinga Wankan Tsarki Ne Lokacin Da Za Ta Yi Kowace Sallah?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Dan Allah ina da tambaya macen da ta yi ɓarin ciki aka mata wankin ciki bayan nan sai jini yake zuwa mata ya dai bayyana jinin ciwo ne. Shin za ta dinga wanka ne lokacin da za ta yi kowace sallah? Ko kuwa tsarki kawai za ta yi lokacin sallah?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

To dan'uwa Za ta yi tsarki kuma ta yi alwala ya yın kowacce sallah, saboda hukuncinsu ɗaya da mai jinin istihala, kamar yadda Annabi Ya umarci Fadimatu 'yar Abi-Hubaish a hadisin Ibnu Hibban mai lamba ta: 1354, da yın alwala yayin kowacce sallah, lokacin da ya tabbatar tana yın jinin cuta.

Don neman karin bayani duba: Risala Fi Dima'u Addabi'iyya: 45

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments