Da yawa 'yan mata da matan aure na halakar da kansu, suna zama mushrikai ta hanyar bin malamai masu yi musu sihiri da manufar taimako.
Mata na zuwa gurin malamai domin neman mallake miji ko
uwar miji ko É—auke hankalin mijinsu daga kan abokiyar zamanta dadai
sauransu, sai dai kuma shi sihiri kafurci ne.
WaÉ—annan da kuke ganinsu kamar
malamai sun tara Alƙur'anai ga manyar carbi da
yawansu ga tarin ƙasa suna duba a kanta suɗin ba malamai ba ne bokaye
ne.
Da yawan 'yan mata suna rasa imaninsu,
suna shirka ta dalilin zuwa gurin malamai da niyyar meman taimako a kan wani
saurayi daga ƙarshe sai ki zama mushrika
baki sani ba.
Duk malamin da kikaje gurinsa dan neman taimako a kan mijinki
ko saurayinki ya ce miki za ai miki aiki to boka ne, ki tashi ki bashi guri.
Domin babu wani aiki da zai miki daya wuce ya baki rubutu
ko wani garin magani ko laya ko ya sa kiyi yanka daga nan kuma sai ki zama
mushtika, da ke da shi duk ku shiga wuta.
Duk malamin da
ki kaji ya ce miki za ai miki addu'a amma da sharaÉ—i, za'ayi yanka, to boka ne,
kitashi ki bashi guri, babu wata addu'a da take da sharaÉ—i sai anmata yanka sannan
ALLAH zai karɓa.
Duk malamin da ki kaje gurinsa neman shawara a kan mijinki
ya ce to ki kawo kuÉ—i kaza ko za ki biya kuÉ—i kaza to ba malamin ALLAH
ba ne ki tashi ki bashi guri, É—an damfara ne.
Malaman sunnah
ba sa karɓar kuɗin kowa, saidai su ɗoraki a kan hanyar da zakibi
ki samo kan mijinki bisa hanyar koyarwar Manzon ALLAH {s.a.w}, ki sami lada
kuma ki sami aljanah kuma ku zauna lafiya da mijinki.
Babu wata addu'a da take da sharaÉ—in sai an yi yanka, shi
yanka idan kina so, bayan kin roƙi ALLAH da kanki a kan wata
buƙata taki ko a kan mijin naki, koma wacce irin bukata
ce, to idan kina da halin da za ki iya yanka duk abin da ALLAH ya azurtaki da
shi na halal sai ki yanka.
Sannan ki dafa abinki ki ci a cikinki yaranki ma suci,
ki aikawa maƙobta suma da niyyar ALLAH ya
biya miki dukkan buƙatunki, wannan kaɗai ya isar miki a gurin
ALLAH {S.W.T}.
Amma kada ki yarda wani malami ya ce a yi yanka kuma
ki yarda, amma a kan kanki ya halatta kiyi babu wanda ya saki ke kika ga dama
kikayi a binki don ALLAH.
Saboda haka ki dafa kowa ya ci da mijinki da 'ya'yanki suci su yi farin ciki
ALLAH zai biya miki buƙatarki saboda dalilin farin
cikin da kika saka mijinki da yaranki.
Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce:
Sadakar da tafi falala ita ce sadakar da aka bada ita
ga É—an uwa tana da lada biyu, ga ladan sadaka ga ladan zumunci.
Sannan ki tashi cikin dare ki kyautata alwala, kiyi
sallah raka'a biyu ki roƙi ALLAH dukkan buƙatunki, musamman a cikin sujadarki ta sallah, sannan ki yanka
duk abin da ALLAH ya hore miki, ki dafa ku ci keda mijinki da 'ya'yanki da niyyar sadaka.
Ko kuma ki sayi alawa ki rabawa yara sadaka don neman
yayewar dukkan damuwarki insha ALLAHU TA'ALAH za ki sami biyan buƙatarki daga ALLAH amma basai kinje wani malami yana cinye
miki kuÉ—i kuma ya jefaki ga aikata shirka ba.
Sannan ya zo cewa duk wanda ya karanta LA'ILAHA ILLAH
ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZ-ZALIMIN sau 40 to ALLAH zai yaye miki dukkan
damuwarki, duk sanda wani abu ya dameki kawai ki zauna ki karanta ta ki miƙa al'amarinki wa ALLAH zakiga biyan buƙata.
Don haka yaku mata ku ji tsoron ALLAH ku kiya yi bin
malaman tsubbu, malaman-nan ba malamai ba ne bokaye ne, kawai neman kuÉ—i sukeyi da ayoyin ALLAH.
Da yawansu sun kafurce, za su iya aikata komai a kan kuÉ—i, wasu daga cikinsu suna
neman matan mutane suce sai ya kwanta da ke sannan za ki sami biyan buƙata, ko kuma ya yi rubutu a jikin azzakarinsa ya kwanta da ke
wannan ai ba ƙaramin kafurci ba ne.
Akwai matan da
sunje gurin irin waÉ—annan mutanen, sun san komai, sun san yadda malaman
suke, basu da kunya ko kaÉ—an, babu tsoron ALLAH a
tattare dasu, ko mutum kike so a kashe miki zai iya kashewa a kan kuÉ—i.
Akwai masu luwaÉ—i da maza, idan namiji yaje neman
taimako sai suce sai an yi luwadi da shi sannan zai sami biyan buƙata.
Wasu kuma sai suce suje su rinƙa neman matansu ta dubura, ba ta farji ba, wannan shi ma umarnin
aljanu ne, kuma ALLAH ya tsinewa wanda ya yi jima'i da matarsa ta dubura da
wanda ya kwant da matarsa tana haila.
Don haka ku rinƙa neman shawara gurin
malaman sunnah su sanar daku hanyoyin da zakubi, ku sami mallakar mazajenku
cikin sauƙi ta hanyar neman yardar
ALLAH, kuma ba tareda kin kashe ko sisi ba.
Ku sani waÉ—annan malaman da yawansu 'yan damfara ne, ku kula sosai, kada su damfare muku imaninku,
su kuma damfare muku kuÉ—a-É—enku.
Kuma ki je ki yi wa mijin naki sihiri idan ALLAH ya sa
mai kula da sallah ne a kan lokacinta wani da ya yi alwala nan take sai sihirin
ya rage ƙarfi koma ya karye.
Idan kuwa ya yi sallah sihirin ya karye, haka dai
zakita yawo kiyita bin bokaye, kinayi yana karyewa harsai kin mutu kina aikata
shirka, kuma ki je ki shiga wuta.
Wasu kuwa suna zuwa sunawa abokan zamansu (kishiya)
sihiri saboda mijinsu ya daina kwana É—akin kishiyarta, ko kuma ya
daina jin daÉ—in kwanciya da ita, ko kuma ya tsaneta ma gaba É—aya.
ALLAH ka bamu ikon aiki da abin da muka karanta.
ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki É—ayanmu Ameen.
**************************************
Wannan É—aya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waÉ—anda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta Æ™arin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.