Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Azumi Da Sallar Dare A Watan Rajab

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Salamu alaikum warahmatullah. Malam don Allah mene ne ingancin yin azumi a watan Rajab?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikumus salam warahmatullah, to Dukkan Yabo ya tabbata ga Allah shi kaɗai.

Da Farko: Shi watan rajab ɗaya ne daga cikin watanni masu albarka wanda Allah ya ce:

“Lallai ne ƙidayayyun watanni a wurin Allah wata goma sha biyu ne (a shekara) a cikin Littafin Allah, a Ranar da Ya halicci sammai da ƙasa daga cikinsu akwai huɗu masu alfarma (na 1, 7, 11, 12 a cikin watanni). Wannan ne addini madaidaici. Saboda haka kada ku zalunci kanku a cikinsu. [Suratul Tawbah ayata 36].

Watannin masu alfarma su ne: Rajab, Dhu’l-Ƙa’dah, Dhu’l-Hijjah da Muharram.

Al- imamul Bukhari (4662) da imamul Muslim (1679) sun ruwaito daga Abu Bakrah (Allah ya ƙara masa yarda) cewa Manzon Allah (SAW) ya ce: Shekara watanni huɗu ne da ita, wanda huɗu daga ciki masu alfarma ne: uku a jere, Dhu’l-Ƙa’dah, Dhu’l-Hijjah da Muharram, da Rajab Mudar wanda ya zo tsakanin jumada da Sha'aban.

Waɗannan watannin ana kiransu da watanni masu alfarma saboda dalilai guda biyu:

1-Saboda an haramta yaki a cikinsu se dai idan maƙiyane suka kawo farmaki.

2-Saboda ƙetare iyaka a cikin watannin masu alfarma shi ne mafi muni a kan kowane lokaci.

Saboda haka Allah ya haramta mana aikata zunubai a cikin waɗannan watannin, kamar yadda ya faɗa:

Saboda haka: “kada ku zalunci kanku a cikinsu.” [Suratul Tawbah ayata 36].

Ko da yake aikata zunubi haramun ne a waɗannan watannin dama wanda basu ba, amma a waɗannan watannin haramcin ya fi karfi.

Al-Sa’di (Allah ya yi masa rahama) ya ce (p. 373): A cikin jumlar “kada ku zalunci kanku a cikinsu.” wakilin suna a nan, za a iya fahimtar cewa yana magana ne a kan watanni sha biyu. Allah Ya ambaci cewa Ya sanya su, su zama ma'auni na lokaci wa bayin sa, wanda za su iya amfani dasu wajen bauta masa, kuma godiya ta tabbata ga Allah game da ni'imarsa.

Wakilin sunan za mu iya fahimtarsa a matsayin watanni huɗu masu alfarma yake nufi, kuma wannan ya haramtawa bayin sa saɓa masa a cikinsu, kamar yadda yake a ko da yaushe haramun ne saɓawa Allah a ciki, saboda haramcin ya fi karfi a wannan lokutan, amman ya fi tsanani a wannan lokutan a kan ko da yaushe.

Abu na biyu: game da tambayarki a kan yin azumi a watan Rajab, wannan kam babu wani sahihin hadisi da ya nuna cewa akwai wata lada ta daban a yin azumi duka ko wani shashe a watan Rajab.

Abin da wasu mutane suke yi, na azumtar wasu kwanaki a watan Rajab, da yin imani cewa su sunfi sauran mutane, wannan bashi da wani asali a cikin shari'a.

Amma akwai ruwaya daga Manzon Allah (SAW) wanda ya nuna cewa Mustahabbi ne yin azumi a watannin nan masu alfarma (kuma Rajab yana daga cikin watannin masu alfarma). Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ku azumci wasu kwanaki daga watanni masu alfarma amma ban da sauran watanni.” Abu Dawood ya ruwaito shi, a hadisi me lamba ta 2428; amma hadisin Albani ya da'ifanta shi a cikin Da’eef Abi Dawood.

To amma ko da wannan hadisin sahih ne wato ya sha, to yana nuna mana cewa mustahabbi ne yin azumi a watanni masu alfarma. Saboda haka idan mutum ya yi azumi lokacin Rajab saboda wannan, kuma sannan ya yi azumi a wasu watannin masu alfarma, to babu komai a kan hakan. Amman ware Rajab shi kaɗai da cewa za'ayi azumi a ciki wannan kuskure ne ba dai dai ba ne!

Shaikhul Islam Ibn Taymiyah (Allah ya yi masa rahama) ya ce a cikin Majmoo’ Fataawa (25/290):

Ga me da yin azumi a watan Rajab kaɗai, to hadisan da suke magana a kan hakan duk basu inganta ba, ballama hadisai ne wanɗanda suke kirkirarru (wato na ƙarya). Malamai basu dogara da ko ɗaya daga ciki ba. ba sa ma daga cikin da'ifan hadisai waɗanda aka ruwaito su, se dai ma mafi yawansu kirkirarrun hadisai ne da karya. a cikin al-Musnad da wasu guraren akwai hadisai da suke cewa Manzon Allah (SAW) yana son yin azuni a watanni masu alfarma, wanda su ne Rajab, Dhu’l-Ƙa’dah, Dhu’l-Hijjah da Muharram, amma wannan yana da alaƙa ne da yin azumi a dukkansu, ba iya rajab ba kawai.

Malam Ibn al-Ƙayyim (Allah ya yi masa rahama) ya ce: Duk wani hadisi wanda ya ambaci yin azumi a Rajab da yin Sallah a wasu dararensa wannan ƙarya ne kuma ƙirkirarran abu ne. Duba al-Manaar al-Muneef, shafi. 96

Al-Hafiz ibn Hajar ya ce a cikin Tabyeen al-‘Ajab (shafi na. 11):

Babu wani sahihin hadisi da za a iya ƙirgawa wanda ya yi magana a kan nagartar watan Rajab, ko wani shashe nasa, ko ba ta wani dare nasa da Sallah.

Shaykh Sayyid Saabiƙ (Allah ya yi masa rahama) ya ce a cikin Fiƙh al-Sunnah (1/282):

Yin Azumi a Rajab be fi yin azumi a wasu watannin ba, se dai cewa yana daga cikin watanni masu alfarma da falala. Babu wata sahihiyar ruwaya a sunna da ta dauka cewa akwai wata falala ta daban a yin azumi a wannan watan. Duk abin da aka ruwaito game da hakan to be inganta da shi ba a matsayin hujja.

Shaykh Ibn ‘Uthaymen (Allah ya yi masa rahama) an tambaye shi game da yin azumi a 27 ga watan Rajab da tsayuwar dare a darenta. Sai ya ce:

Yin Azumi a 27 ga watan Rajab da tsayuwar darenta da Sallah bidi'a ne kuma ko wace bidi'a ɓata ce.

Majmoo’ Fataawa na Ibn ‘Uthaymeen, 20/440.

Kuma Allah ne mafi sani.

📚Shashen Fatawa bisa Ƙur'ani, Sunna da Maganganun Magaba ta na ƙwarai.

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments