Shayarwa

    Wannan na ɗaya daga cikin jerin waƙoƙin Malam Khalid Imam da a kullum suke faɗakarwa da ilimantarwa da nishaɗantarwa. Yana taɓo fannoni daban-daban a cikin waƙoƙinsa, ciki har da abubuwan da suka shafi lamuran yau da kullum.

     

    ÆŠan uwana ga nasiha,

    Azumi ya zo ka shayar.


    In kana da hali da iko,

    Kar kai sakaci ka shayar.


    Rijiyar bohol ginata,

    In kana da hali ka shayar.


    Sadaka ce mai gudana,

    Rijiya ka gina ka shayar.


    Wanda bai da hali da ƙarfi,

    Kar yai sakacin ya shayar.


    Ko da moÉ—a guda ne,

    Na ruwa dage ka shayar.


    Hadisai sun bayanai,

    Falala ta ruwa mu shayar.


    Ƙorama kogi da kafki,

    Rabbana Ya yi don Ya shayar.


    HaÉ—in gwiwar mutane,

    Alheri ne su shayar.


    Manzon rahama a fili,

    Yai bayani don mu shayar.


    Hanyar aljanna É—oÉ—ar,

    Mu ba da ruwa mu shayar.


    Wata karuwa mai dabara,

    Kare ta gani ta shayar.


    Zunubanta kakaf Ya yafe,

    Duk da ma dabba ta shayar.


    Ko 'yan wuta ran ƙiyama,

    Kukansu guda a shayar.


    Da su ko za su tsira,

    Yunwarsu fa su a shayar.


    Ruwa dai rayuwa ne,

    Allahu Ka sa mu shayar.


    Yau ga Ramadana ya zo,

    Ka ba da ruwa ka shayar.


    Leda ta fiya wata ce?

    Ko da É—aya ce ka shayar.


    A shayarwa da romo,

    Su kiyashi ma mu shayar.


    Duka dabbobi mu duba,

    Da idon rahama mu shayar.


    Sadaka mui wa iyaye,

    Ta ruwa domin mu shayar.


    Rijiyoyi ƙauyukanmu,

    Mu je mu gina mu shayar.


    Guzuri za kai wa kanka,

    Ruwa muddin ka shayar.


    Wasu ga su suna da damar,

    Wai ba sa son su shayar.


    A gidansu suna da bohol,

    Mata su hana su shayar.


    Wai ba sa son gidansu,

    A É“ata don a shayar.


    Ba wauta ba asara,

    Ta irin mai ƙin ya shayar.


    Malam Khalid Imam
    08027796140
    khalidimam2002@gmail.com

    14/03/2023

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.