Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mene ne hukuncin wanda ya ga wani ɓangare na jikin matarsa ko
ya sumbace ta (kissing) ko kuma ya kalli wassu finafinai na tsiraici,
sai maziyyi ya fito masa alhali yana azumi? Allah ya sama iliminku albarka.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Fitan maziyyi ba ya lalata azumi a maganar da ta fi inganci daga cikin
maganganun maluma guda biyu, lamarin haka ya ke sawa'un ya fita ne saboda sunbantar
mata, ko kuma ta hanyar kallon finafinai, ko kuma makamantan haka, daga cikin
abubuwan da su ke ta da sha'awa, Sai dai kuma baya halatta ga musulmi ya kalli
finanan tsiraici da batsa, ko kuma sauraron abin da Allah ya haramta na
sauraron waqoqi, ko kayan kade-kade.
Amma fitar maniyyi da sha'awa yana lalata azumi;
sawa'un hakan ya auku ne sakamako runguma ko sumbanta ko maimaita kallo, ko
makamancin haka daga cikin sabbuban da su ke ta da sha'awa; Kamar wasan fitar
da maniyyi (istimna'i), da makamancinsa.
Mafarki da tunani, su kuma azumi ba ya ɓaci da su, ko da kuwa
maniyyi ya fita da sababinsu.
DUBA FATAWA ISLAMIYYAH, MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT
MUTANAWWI'AH, (15/ 267).
Allah ta'ala yasa mudace
Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa
Tare Da Fadakarwa a Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BJikpGm7VXV1vEVVGcNH5J
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.