Maziyyi shi wani ruwa ne fari, bashi da kauri kuma yana da danƙo/yauƙi, yana fita ya yin da mace da namiji suka gabatar da wasa, ko kuma tunanin jima'i, ko kallon batsa ko karanta wani rubutu na batsa.
Sannan ba a jin mutuwar jiki bayan fitarsa, wani lokacin ma ba a sanin lokacin da yake fita.
Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce:Da Aliyyu ɗan Abu Ɗalib (R.A) lokacin da ya yi masa tambaya game da Maziyyi, ya
ce masa: Ka wanke gabanka, ka sake alwala
[Bukhari da Muslim].
WADIYYI: Shi wani ruwa ne fari kamar farau-farau, mai
kauri, yana fita bayan fitsari.
Amma mafi akasarin dalilin fitowarsa ciwo ne, sanyi ne yake kawo shi,
shi ma yana ɗaukar hukuncin tsarkin fitsari.
MANIYYI: Wani ruwa ne fari, mai kauri, yana fitowa
tare da sha'awa, yana tunkuɗar juna, ana samun mutuwar
jiki bayan fitarsa, yana wari irin warin bara-gurbin ƙwai.
Sannan kuma maniyyi mai tsarki ne, domin da najasa ne
da Manzon ALLAH {s.a.w} ya yi umarni a wanke shi.
Ana wanke shi idan yana ɗanye, idan ya bushe kuma, to
kawai sai a kankare shi.
Saboda hadisin Nana A'isha (R.A) ta ce:
Manzon ALLAH {s.a.w} ya kasance yana wanke maniyyi,
sannan ya fita zuwa sallah da wannan tufar, ina ganin gurbin wurin da ya wanke.
[Bukhari da Muslim].
A ruwayar Muslim kuwa cewa tayi: Na ganni ina kankare
shi maniyyin daga tufar Manzon ALLAH {s.a.w} sannna ya yi sallah da wannan
tufar.
[(Bukhari da Muslim].
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
Post your comment or ask a question.