Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina ne ya yi tafiya da zai dawo bai yi azumi ba shi ne yake ce min wai in ajiye azumi yana da buƙatata nace a'a shin na yi laife?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mijina ne ya yi tafiya da zai dawo bai yi azumi ba shi ne yake ce min wai in ajiye azumi yana da buƙatata nace a'a shin na yi laife?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To baiwar Allah hakika ba ki da laifi kuma kin kyauta muna fatan Allah zai baki lada mara adadi sakamakon rashin amincewa mujinki da kikayi a irin wannan lokacin na Ramadan, sabida haka ko a wane lokaci kar ki amince wajen yiwa mijin bayiyya wajen saɓawa Allah haramunne a yiwa miji biyayya domin a saɓawa Allah mahalicci.

A ƙarshe kuma lallai shi wannan mijin ya ji tsoron Allah don kawai ba ya azumi sakamakon tafiya be kamata ya hallakar da matar ta hanyar umartarta da aikata saɓon Allah ba, Kai da akace ka tseratar da iyalinka daga halaka me yasa kake kokarin hallakar da ita da kanka.

WALLAHU A'ALAM

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BpO6i5KwGBm8IcVtlhBr0j

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments