Ticker

6/recent/ticker-posts

Bayani Game Da Sujada Ƙabli Da Ba’adi 01

• Anayin sujjadu biyu kafin sallama (ƙabli) idan aka yi ragi bayan angama tahiya a sallah.

• Anayin sujjadu guda biyu bayan sallama (Ba'adi) idan aka yi ƙari a sallah.

SHARHI:

 Idan mutum ya yi ragi a cikin sallah, bayan ya yi tahiyarsa ya gama, ya yi wa Annabi {s.a.w} salati da duk wata addu'a da akeyi a bayan tahiya, to ba zai yi sallama ba,

 Sai ya ƙudurci niyya a cikin zuciyarsa na sujjada ƙabli, sai ya yi sujjada guda biyu bayan ya gama sujudun sai ya yi sallama shi ke nan, ba zai sake wata tahiyar ba, kawai sallama zai yi.

 Wanda kuma ya yi ƙari a cikin sallah, bayan ya yi tahiya ya yi wa Annabi {s.a.w} salati da duk wata addu'a da akeyi bayan tahiya,

 Sai ya yi sallama sannan kuma ya ƙulla niyya a cikin zuciyarsa na ba'adi, sai ya yi sujada guda biyu, idan ya gama sai ya yi sallama kawai basai ya sake wata tahiyar ba.

• Wanda ya rage ya kuma yi ƙari, ya yi sujjada kafin sallama (ƙabli).

SHARHI:

 Wanda ya yi ragi ya kuma yi ƙari a lokaci guda a cikin sallah to ya yi sujjada ƙabli.

Misali:

Mutum ne yana sallah mai raka'a huɗu, bayan ya sallaci raka'a biyu a maimakon ya zauna ya yi tahiya, sai ya manta ya miƙe, bayan ya miƙe sai kuma ya tuna yadawo ya zauna,

 To wannan miƙewa da ya yi ita ce ragin da ya yi, dawowar da ya yi kuma bayan ya riga ya miƙe gaba ɗayansa, ya rabu da ƙasa, to shi ne ƙarin da ya yi, ya zama ragi da ƙari a lokaci ɗaya, a nan ƙabli ta kamashi, wato sujjada biyu kafin sallama.

• Wanda ya manta sujjada ƙabli har ya yi sallama, to ya yi sujjada idan ya kasance a kusa.

• Idan ya tsawaita, ko ya fita daga masallaci sujjadar ta ɓaci, sallah tana ɓaci tare da ɓacin sujjada, idan ta kasance a bisa sunnoni guda uku ko fiye da haka, idan ba haka ba, ba ta ɓaci ba.

SHARHI:

 Idan mutum sujjada ba'adi ko ƙabli ta kamashi, sai ya manta baiyi ba, saida ya gama sallarsa duka, sai ya tuna, to ya yi ta a lokacin daya tuna,

 Idan kuma ya manta baiyi ba, har ya fita daga masallaci har ma ya yi nisa dashi, indai abin da ya tauye yakai sunnoni uku ko sama da haka to sallarsa ta ɓaci.

• Wanda ya manta sujjada bayan sallama (Ba’adi) to ya yi sujjada ko da bayan shekara ne.

SHARHI:

 a nan malam yana nufin idan mutum ba'adi ta kamashi, sai kuma ya manta baiyi ba, to ko da bayan shekara ɗaya ne ya tuna, sai ya ramata nan take, sai dai a zance mafi ƙarfi, basai ya ramata taba.

• Wanda ya rage farilla sujjada baza ta wadatar masaba a gareta.

SHARHI:

 Idan mutum ya manta wani rukuni a sallah, farillah ke nan, kamar ruku'u ko sujada ko karatun fatiha, to dole sai ya ramasu, iya sujada ƙabli ko ba'adi ba ta ɗauke masasu.

• Wanda ya tauye mustahabi babu sujada a gare shi.

SHARHI:

 Idan mutum ya manta mustahabi wato kamar: faɗin Rabbana walakal hamdhu a bayan liman ko wanda yake sallah shi kaɗai, ko ɗaga hannu a ya yin kabbarar harama, ko wanda ya manta addu'a a cikin ruku'u ko sujada, duk wannan ba'ayi musu sujada don an mantasu.

 • Sujjadar ƙabali ba ta kasancewa sai da barin sunnoni guda biyu ko fiye da haka.

  Amma barin sunna guda ɗaya ba a yimata sujjada, sai dai idan ɓoyewa da bayyanawane na karatu.

 SHARHI:

  Idan mutum ya manta sunna ɗaya tak, a cikin sallah, baya zama wajibi akansa sai ya yi sujada ƙabli ko ba'adi, sai dai idan sunnoni guda biyu ya rage.

  Amma idan mutum ya ɓoye karatu a inda ake bayyanawa to sujjada ƙabli ta kamashi, idan kuma ya bayyana a inda ake ɓoyewa to sujjada ba'adi ta kamashi.

 ALLAH shi ne mafi sani.

 ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

 

Duk mai neman ƙarin bayani ya yi mana magana ta private.

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments