Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Ba Ya Azumi Sai Ya Ga Wata Da Idonsa.

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Salamun alaikum, Dr. Tambaya ce aka jefa mani ina gabatar da darasi wa mata a garin Firji: mace ce mijinta bai yarda ya ɗauki azumi ba sai ya ga wata da kansa (bai yarda da sanarwar Sarkin Musulmi ba), to inda mushkilar take shi ne, ita matarsa ta yarda da sanarwar Sarkin Musulmi amma sai ya ce kada ta kuskura ta dauki azumin, to shin minene matsayinta? Domin ta ajiye azumin saboda tsoron kada ya wulaƙanta ta.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam A Zahiri ba za ta masa biyayya a nan ba, Tun da Azumi rukuni ne daga cikin ginshikan musulunci.

Annabi SAW yana cewa:

إنما الطاعة في المعروف

Ana yiwa jagora biyayya ne idan ya yi umarni da abin da ya dace da sharia"

Sannan yana cewa: "Ana yin azumi ne ranar da mutane suke yin azumi"

Allah ne mafi sani

Amsawa🏻

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments