Hukunce Macen Ta Sami Tsarki Bayan Fitowar Alfijir

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Idan mace ta sami tsarki bayan fitowar Alfijir, Shin zata kame baki awannan yinin? Ya zamana ta azuminci wannan yini kenan ko Kuma ramuwar wannan yinin yana kanta, bayan ta kuma kame bakinta?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Idan mace ta sami tsarki bayan fitowar Alfijir malamai suna da maganganu guda biyu gameda kame bakinta a wannan yinin;

    1. Magana ta farko:- Hakika an dora mata kame baki a ragowar wannan yinin, sai dai shi (Kame bakin) ba za a kirga mata shiba, wajibine sai ta rama azumin wannan yinin. Wannan shi ne fitaccen zance a Mazhabar Imamu Ahmad Allah yayi masa rahma.

    2. Magana ta biyu:- Hakika ba'a dora Mata kame bakin ragowar wannan yinin ba, saboda azumi acikin wannan yinin bai halasta ba agareta, kasancewar afarkonsa tana cikin haila, dan haka azumin bai inganta mata ba, kame bakinta bashi da wani fa'ida, wannan lokacin lokacine da bashida wani hurumi agurinta, saboda an umarceta da taci ta Sha acikin farkon ranar, kai barima an haramta mata azumtar sa a farkon Ranar

    Azumi a Shari'a shi ne :

    Kamewa daga ciye-ciye da shaye-shaye dan bautawa Allah mai girma da buwaya daga fitowar Alfijir har zuwa faduwar rana.

    Wannan zance kamar yadda kake ganinsa shi ne zance mafi inganci daga cewa sai an kame baki,

    A bisa zantukan duka biyu sun yi ittifaƙi akan wajabta mata rama azumin wannan yinin".

    📝 المصدر :

    [ ٦٠ سؤالا في أحكام الحيض والنفاس/لفضيلة الشيخ محمد بن صالح العثيمين رحمه الله ص٧].

    Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    ************************************** 

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.