Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene ne Hukuncin Ɗaukar Mace Aikin Soja?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne Hukuncin Ɗaukar Mace Aikin Soja?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Ba ya halatta ɗaukar mace aikin soja, domin mace ba ta cikin masu (ɗaukar makami su yi) jihadi." "Wannan dai kallafa mata wani aiki ne wanda ba ta iyawa, sannan kuma bijiro da ita ne zuwa ga wata fitnah da kuma sharri." " Sannan kuma kamar ana so a fitar da ita ne daga matsayin ta na ɗiya mace ne; da kuma dora mata aikin da maza suka keɓanta da shi ne, wannan kuwa baya halatta." " Wannan aikin kafirai ne, amma ba aikin musulmi ba ne, domin su musulmi basu sanya mata aikin soja." " Waɗanda dai kawai suke irin wannan aikin su ne kafirai, ko kuma wasu kasashen Larabawa waɗanda suke kwaikwayon kasashen kafirai daga cikin (kasashen Larabawa) Yan Gurguzu ( Socialists), da kuma kasashen Larabawa wadanda Jam'íyyar Ba'ath ke mulkarsu, da dai sauran su."

ABUBUWAN LURA a nan:

Duk a cikin tarihin musulunci, babu inda aka nuna cewa mata suna shiga aikin soja, tare da cewa suna fita zuwa jihadi tare da sauran sojojin musulunci,

amma ba don su yi aikin soja ɗin ba. A'a suna dai bada gudummuwa ne a wajen bada taimakon gaugawa kamar jiyar waɗanda suka samu raunuka da sauran ayyukan jin kai idan akwai bukatar haka ɗin . Shi aikin soja, aiki ne wanda a Sharí'ah ta musulunci ya keɓanta ne kawai ga maza, amma ban da 'ya'ya mata. Ɗaukar mata aikin soja Saɓawa dokar Allah ne , domin Allah Subhanahu wa Ta'ala Ya hana buɗe duk wata kafa da za ta kawo cakudar maza da mata , wadda kuma za ta iya haifar da fitnah mai girma kamar irin wannan aikin soja ga mata. Duk mutumin da ya goya wa ɗiyarsa baya ta shiga aikin soja, ko kuma ya nema mata conscription (damar a ɗauke ta aikin soja) , to babu ko shakka ya saɓawa umarnin Allah da Manzon Sa Baya halatta musulmi su yi koyi da kafirai a irin waɗannan wuraren , domin ko shakka babu sai sun haddasa fitintinu na saɓon Allah waɗanda ba za su iya lisaftuwa ba. Shi daukar mace aikin soja , ba komi ba ne ba face cin mutuncin ɗiya mace.

WALLAHU A'ALAM

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments