Ticker

6/recent/ticker-posts

Mata Guda 10 Wanda Allah Ya Tsinewa Kuma Ba Zai Kalle Su Kallon Rahma Ba A Ranar Alƙiyama

 1• Mata masu tsaga fuskokinsu.

Ma'ana: Masu zane da wuta ko wani abu, zanen da ba zai goge ba har abada amma ban da zanen fulawa.

2• Mata masu aske gashin gira.

Ma'ana: Masu aske girarsu domin kwalliya, su ne masu aske gefenta a yi ta mata wani irin gyare-gyare.

3• Mata masuyin wushirya.

Ma'ana: Masu zuwa su tsaga haƙorinsu domin su yi wushirya.

4• Mai ƙarin gashi da wacce ake ƙara mata gashin.

Ma'ana: Waɗanda suke ƙara gashinsu da wani gashi da kuma masu yi musu ƙarin gashin.

 

5• Matar da mijinta ya yi fushi da ita.

Ma'ana: Matar da take ɓatawa mijinta rai ba tare da hakki ba, tana sakashi ɓacin rai.

6• Mata masu shigar maza.

Ma'ana: Mata masu saka kayan maza, kayan da maza ne ke amfani dasu amma sai mace ta zo ta saka, ko kuma ta rinƙa ɗabi'u irin na maza.

7• Mata masu yawan ziyartar ƙabur-bura (maƙabarta).

Ma'ana: Mata masu yawan zuwa maƙabarta ziyara akai-akai.

8• Mata masu kururuwa a kan mamaci.

Ma'ana: Matan da idan an yi mutuwa sai suzo suyita ihu suna kuka suna cewa sun shiga uku, a maimaikon su nemawa mamaci gafarar ALLAH.

9• Mata masu auren kisan wuta.

Ma'ana: Mace ta yi auri da wani namiji da sanin shi tsohon mijin nata, ko kuma da sanin shi wanda ta aura ɗin donta koma gidan tsohon mijinta ita ma wannan ALLAH ya tsine mata,

Sai dai ya halatta ta auri wani namiji da niyyar za ta nemi saki daga baya domin komawa gidan tsohon mijinta amma ba za ta sanar shi wanda za ta aura ba, kuma ba za ta sanar da tsohon mijinta ba, kawai dai za ta ƙudurce ne ta ɓoye iya ita laɗai a cikin zuciyarta, kamar yadda hakan ya zo a hadisi.

10• Mata masu bayyana tsiraicinsu.

Ma'ana: Matan da suke saka kaya masu ɗame jiki, zakaga ga kayan an saka amma kuma sun ɗame jikinsu ana ganin shatar komai na jikinsu,

 Ko kuma mace ta saka kayan da sukeda shara-shara ko mace ta fito waje ana. ganin ƙafarta a wajen ba ta saka zani ya rufe har kafarta ba, ko ta saka safa, wata ma har ƙaurinta ake gani.

 Hadisi ya tabbata daga babban sahabin Manzon ALLAH {s.a.w} wato:

 Abdullahi Bin Mas'ud (R.A) ya ce:

ALLAH ya tsinewa mata masu sawa a yi musu zanen shasshawa (zane a jiki da wuta) da masu yi musu zanen,

 Da masu aske gashin girarsu, da masu tsaga wushirya don su yi kyau, alhali asali basuda ita.

[Sahih Bukhari 5587]

[Sahih Muslim 5538]

 Amma fa haramcin zanen bai shafi zane na fulawa da mata suke yi ajikinsu domin kwalliya wa mazansu ba.

 Kamar yadda bayanin hakan ya zo cikin Tafsirin Kurthubiy Juzu'i na biyar shafi na 393.

 

 Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce:

Yaku taron mata ku yi sadaka, kuma ku yawaita neman gafarar ALLAH domin lallai ni naganku

mafiya yawanku 'yan wuta ne.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu.

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments