Ticker

6/recent/ticker-posts

Laulayin ciki ya sa ina waiwaye a sallah, yaya sallata?

Manzon ALLAH {s.a.wa} Yana cewa:

Waiwaye a sallah wani faucewa ne da Shaiɗan yake fauta daga sallar mutum.

kamaryadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lambata: 718.

 Malamai suna cewa waiwaye a sallah makaruhi ne saboda hadisin daya gabata.

 Waiwaye yana halatta idan akwai buƙata, saboda akwai lokacin da sayyidina Abubakar (R.A) ya faralimanci, saboda Manzon ALLAH {s.a.w} baya nan,  Bayan Annabi {s.a.w} ya dawo sai ya shigo masallaci, sahabbai suna ganinsa sai suka fara tafi, sai sayyadina Abubakar (R.A) ya waiga lokacin da ya ji tafi ya yi yawa, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisimai lamba ta: 2544.

 Malamai suna cewa: Waiwayan da Abubakar (R A) ya yi yana nuna hallacin yin waiwaye saboda buƙata, tun da Annabi {s.a.w} baimasa inkari ba.

 Don neman ƙarin bayani duba: Fatawa

Nurun Aladdarb 9/225.

A bisa abin da ya gabata, ya hallata ki ringa yin waiwayesaboda zubar da yawun da ya zama larura, sai dai duk abin daaka halatta saboda buƙata, ba a so a wuce gwargwadonta

ALLAH shi ne mafi sani.

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments