Ticker

6/recent/ticker-posts

Lokacin Karɓar Addu'a A Ranar Juma'a

 Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mlm ya aiki to ALLAH saka muku da alkhari. Mlm tambayana shi ne don Allah an ce addu'a ranan Juma'a karɓebe ne shi ne nake so amun karin bayani kuma dawani lokaci ne ya fi cancanta.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Ranar juma’a tana da wani lokaci na musamman da Allah yake amsar addu’o’in bayinsa a cikinsa. Annabi s.a.w ya bayyana haka:

Annabi s.a.w ya ambaci ranar juma’a sai ya ce: (a cikinta akwai wani lokaci da babu wani bawa musulmi da zai dace shi, yana Sallah yana rokon Allah a cikinsa wani abu, face Allah ya basa). “Qudaibata ya kara a cikin riwayarsa, sai Annabi s.a.w ya yi nuni da Hannunsa yana nuna lokacin kaɗan ne”

@Bukhari da Muslim da Malik a Muwaddha da Ahmad.

Malamai sun yi saɓani akan wani Lokaci ne wannan:

Ibn Qayyim R.A yana cewa: “Malamai sun yi saɓani akan wannan lokacin na ranar juma’a,an sami maganganu guda goma”.

@Zadul Ma’ad.

Amma maganar da tafi karfi a cikin gomar magance guda biyu:

1-Daga hawan Liman kan Mumbari zuwa kare Sallah.

Dalili akan wannan shi ne:

Abinda Imam Muslim ya ruwaito a cikin Littafinsa daga Hadisin Abi Buraidah bn Abi

Musa: Lallai Abdillahi dan Umar R.A ya ce da shi: Shin kaji babanka yana bada Hadisi daga Annabi s.a.w akan Lokacin Amsa addua a ranar juma’a??? Sai ya ce EH: Na ji shi yana cewa: naji Annabi s.a.w yana cewa: (Shi ne tsakanin Zaman Liman akan Minbari zuwa kare Sallar juma’a).

@Mulim.

2-Bayan Sallar La’asar: Kuma Malamai sukace wannan magana itace mafi rinjayen magana. Ita ce maganar Abi Huraira R.A da Abdillahi Bn Sallam R.A da Imam Ahmad da sauran Malami da dama. Hujjarsu ita ce: Daga Abi Sa’I’d da Abi Hurairata R.A suna cewa: Lallai Annabi s.a.w yace: (Lallai a ranar juma’a akwai wani lokacin da babu wani bawa musulmi wanda zai dace da wannan lokacin yana rokon Allah alkhairi a cikinsa face sai Allah ya bashi, shi ne bayan Sallar La’asar).

@Ahmad

A hadisin Jabir bn Abdiilah R.A Annabi s.a.w yace: (Ku nemi wannan lokacin a sa’ar karshe bayan SallaR La’asar).

@Abu Dauda da Nisa’I.

Allah ne mafi sani.

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DVpHjgfRdK9IRWvkB23lbE

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Post a Comment

0 Comments